Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ana zargin shugaban makaranta da laifin yi wa dalibarsa ’yar shekara 4 fyade

Ana  zargin Abubakar Haruna shugaban makarantar August Nursery and Primary School da ke Unguwar Jaba a Karamar Hukumar Sabon Gari Jihar Kaduna da yi wa dalibarsa ’yar shekara hudu fyade (an sakaya sunanta) a harabar makarantar.

Mahaifin yarinyar mai suna Ibrahim Salisu ya yi wa Aminiya bayani cikin damuwa yadda lamarin ya faru kamar haka: “A ranar Juma’a 7 ga watan Yuni da misalin karfe goma na safe muna zaune a gida sai aka fara nemanta don a yi mata wanka amma ba a ganta ba, nan da nan muka bazama neman inda ta shiga sai muka ga kofar makarantar su a bude da ma makarantar tana kusa da mu ne kuma ana hutun sallah a wannan lokacin, to sai muka shiga makarantar domin mu duba, muna shiga sai shi malamin mai suna Abubakar Haruna da ya ji motsi sai ya haura katanga ya gudu inda muka tarar da yarinyar tawa tare da wani yaro, wai ya kira su ne zai ba su goron sallah, domin yaran duk dalibansa ne na  ajin (Nursery) da ke makarantar.”

ADVERTISEMENT

A nan ne muka tarar da yarinyar tawa cikin wani mummunan yanayi saboda ya bata mata jiki da maniyyi sai kuka take yi.  Da muka daga ta ba ta iya tafiya sai muka kai ta ofishin ’yan sanda da ke Kasuwar Mata a Sabon Gari  daga nan ne aka ba mu wasu ’yan sanda aka taso keyar malamin.  Abin mamaki bai musanta laifin da ya aikata ba  inda ya ce lallai ya aikata laifin kuma aikin shaidan ne.

Mahaifin  yarinyar ya kara tabbatarwaAminiya cewa,  da ’yan sanda suka gudanar da binceken su sai suka tura mu Asibitin su mai suna Police Clinic da ke MTD Police Station Sabon Gari, inda suka gudanar da nasu binciken a likitance kuma duk a wannan ranar ce muke ta zirga zirgar, kuma na biya asibitin Naira dubu 14 domin a yi binceken yarinyar tawa, to bayan sun kammala gwaje gwajen da suka yi sai suka ce an yi sa a bai yi wa yarinyar rauni sosai ba amma  sauran gwaje-gwajen sun ce mu dawo ranar Litinin mu karba.

ADVERTISEMENT

Mahaifin yarinyar ya ce, ba abin da ya fi tayar masa da hankali sai ganin cewa  malaminta ne ya aikata wannan aiki, kuma shi Abubakar Haruna abokin karatunsa ne a wannan makarantar domin ajinsu daya. “A wannan makaranta muka kammala karatummu, idan da aminci ai  kamar a matsayin mahaifinta yake don haka na damu kwarai, kuma zan  tsaya sai na ga an dauki matakni hana faruwar haka nan gaba.

“Ina kira ga Hukumar Kare Hakkin  Kananan Yara su shigo cikin lamarin su sa ido domin kwato wa ’ya ta hakkinta.”

Aminiya ta ziyarci makarantar August Nursery, Baby Care and Primary School da ke Unguwar Jaba inda Daraktan makarantar August Olema ya ce, “Ina gona a ranar, dominn ana hutun Sallah sai wani makwabci na malamin makarantar allo ya kira ni in dawo gida akwai matsala a makaranta, to nan da nan na dawo, ko da na dawo har an kama Abubakar Haruna an kai shi ofishin ’yan sanda,kuma ya tabbatar  ya aikata wa yarinyar fyade, ka ga a matsayina na Kirista ai addinina bai yarda da haka ba kuma ni malamin makaranta ne kuma wannan makarantar ta dade muna zaune lafiya da jama’ar unguwar, kuma shi Abubakar Haruna wanda ya yi wannan laifin da mahaifin yarinyar Ibrahim Salisu ajinsu daya duk wannan makarantar suka yi  don haka tun a ofishin ’yan sanda  na dauki matakin korarsa daga aikin koyarwa a makaranta, kuma na yi taro da iyayen yara da makwabta na, kuma mun fahimci juna.”

Aminiya ta zanta da wasu daga cikin makwaftan makarantar inda suka yi Allah wadai da abin da  malamin  ya aikata, kuma suka ce da ma ana masa zargin hakan sai yanzu ne asirinsa ya tonu.

Da Aminiya ta ziyarci ofishin ’yan sanda da ke Kasuwar Mata a Sabon Gari ta iske DPO ba ya nan sai Mataimakinsa DCO Abubakar Ibrahim wanda ya roki  a yi hakuri har sai DPO ya dawo don maganar tana hannunsa.

Aminiya ta tuntubi Kakakin rundunar ’yan sanda na Jihar Kaduna ASP Yakubu Sabo ta waya amma ba ta same shi saboda matsalar yanayi (network).