✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin wata da sheka wa mijinta da amaryarsa  ruwan zafi

An gurfanar da wata mata mai suna Maimuna Danlami a gaban Kotun Majistare da ke Hajj Camp bisa zarginta da sheka wa  mjinta da amaryarsa…

An gurfanar da wata mata mai suna Maimuna Danlami a gaban Kotun Majistare da ke Hajj Camp bisa zarginta da sheka wa  mjinta da amaryarsa ruwan zafi a lokacin da suke barci.

Mai gabatar da kara ya shaida wa kotu cewa  matar mai suna Maimuna Danlami ta sheka wa mijinta da amaryarta ruwan zafi ne sakamakon tsananin kishi da ya turnuke ta.

Sai dai wadda ake zargi ta musanta laifin da ake zarginta, laifin da mai gabatar da kara ya ce ya saba wa sashe na 342 na Kundin Shari’a na Final Kod.

Alkalin Kotun Mai shari’a Sakina Aminu ta bayar da umarnin tsare wadda ake zargin a kurkuku kuma ta dage sauraren karar zuwa yau Juma’a.