✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zarginsu da almundahanar man dizel na Naira miliyan 44

An gurfanar da wadansu yan kasuwa a gaban Kotun Majistare ta 35 da ke Nomansland a Kano bisa zarginsu da yin sama da fadi da…

An gurfanar da wadansu yan kasuwa a gaban Kotun Majistare ta 35 da ke Nomansland a Kano bisa zarginsu da yin sama da fadi da wasu tankokin man dizEl guda bakwai da kudinsu ya kai Naira miliyan 44 da rabi mallakar Kamfanin Dangote da aka dauko daga  Kalaba, Jihar Kuros Riba da niyyar sauke shi a jihohin Kano da Legas.

Mai gabatar da kara, Sufeto Nura Mukhtar ya shaida wa kotun cewa  wani mai suna mai Faruk Tijjani Zawiyya dan Unguwar Koki a Jihar Kano da ke aiki a Kamfanin Dangote ya amince wa wani da ake kira Bello Balarabe Mohammed da ke Legas ya dauki motocin dizel din don kai su jihohin Legas da Kano.

Takardar karar ta ce  “Sai dai bayan dan kasuwar ya karbi wannan dizel lita dubu 235 sai ya hada baki da wani mai suna Jafar Inusa da Abdullahi Alhaji Haladu suka karkatar da tankokin dizel din tare da mallake kudin baki daya.”

Sai dai dukan wadanda ake zargi sun musanta laifuffukan na hadin baki da zamba cikin aminci da gaza alkinta dukiya da cuta, laifuffukan da suka saba wa sashe na 97 da na 313 da na 309 da na 320 na Kundin Final Kod.

Alkalin Kotun Mai shari’a Sanusi Usman Atana ya yi umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake zargi a ofishin ’yan sanda tare da dage shari’ar zuwa lokacin da ’yan sanda za su gama bincikensu kasancewar za su tafi har garin Kalaba don gudanar da bincike a kan lamarin.