Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ana zaton wuta a makera…

A yayin da zaben shekarar 2019 yake ta kara karatowa yanzu sai samun rigingimu ake yi nan da can wadanda suka shafi kabilanci da addini.

An yi kashe-kashe da dama a kasar nan wadanda ake danganra su da addini da kabilanci tun da kasar nan ta koma mulkin demokadiyya daga shekarar 1999 zuwa yanzu, duk wadannan rikice-rikicen ana taso da su ne domin cim ma burin siyasa kawai

ADVERTISEMENT

Talakawa su ne ake tunzurawa suna kashe kawunansu, inda haka kawai suna zaune lafiya da junansu sai a wayi gari suna ta kashe junansu tare salwantar da dukiyoyinsu, su kuma manyan ‘yan siyasa suna can gefe guda suna kallo, sai dai su rika surutai a kafafen watsa labarai.

Yanzu a manyar da kashe rai ba a bakin komi ba a kasar nan, haka kawai sai a wayi gari an fada wa wata al’umma da kisa, misali, irin kisan kiyashin da aka wa makiyaya a yankin Mambila a jihar Taraba, inda rahotanni suka nuna cewa an kashe mutane dubbai tare da kashewa da kona dubban dabbobi. An yi zargin cewa har naman mutane aka rika gasawa ana ci a wannan rikicin.

ADVERTISEMENT

Haka kawai domin cim ma wani buri na siyasa aka dauki karar tsana aka dora wa fulani makiyaya wanda ya sanya aka mayar da rayukansa ba a bakin komi ba a kasar nan.

A jihar Ekiti lokacin Gwamna Fayose aka fara kafa dokar hana kiwo na yawo da dabbobi, aka ce dole sai dai a samu wuri guda a yi kiwo, alhali ba a samar wa makiyaya da wurin ba. Haka nan aka sanya fulani makiyaya a jihar Ekiti a gaba ana ta cin zarafinsu.

Daga nan sai jihar Binuwai ta dauka, inda a nan ma aka kafa dokar haramta kiwo na yawo da dabbobi ba tare da taimaka wa masu kiwon  da yadda za su samu sauki ba, a sakamakon haka aka yi ta kashe makiyaya da sunan rikicin makiyaya da manoma, sai.wadansu kabilu su je su kashe wadansu sai a ce fulani ne domin a samu damar kashe su, shi ya sanya aka mayar da ran bafilatani a jihar Binuwa kamar na kiyashi, duk inda aka  hadu da shi sai kisa, akwai lokacin da aka kashe wadansu fulani cike  da mota a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani biki.

Haka nan an yi irin wannan kashe-kashen na fulani a jihohin Nasarawa da Filato da kudancin Kaduna. Kuma abin mamaki shi ne wadansu kafofin yada labarai da shugabannin addini ne suke ruruta wutar rikicin.

Al’amarin ya fi bayar da mamaki da ya kasance shugabannin addini su ne suke kokarin tayar da fitina maimakon taimakawa a kwantar da ita.

A ‘yan kwanakin ma an yi ta yayata wadansu hotunan bidiyo da ke nuna wadansu shugabannin addini suna zuga mabiyansu domin su tayar da hargitsi. Misali na baya-bayan ne shi ne hoton bidiyon wani limamin coci da aka nuna.yana karaji yana bayyana wa masu ibada da suka taru a cocin nasa cewa gwamna Nasiru el-Rufa’i ne ya fara kakaba  wa mutane dokar hana fita dare da rana, inda ya ce an yi haka ne domin a musguna masu. Alhali gwamna Patrick Yakowa shi ne wanda ya fara kakaba wannan dokar a lokacin da hargitsin da ya tashi bayan zaben gwamna da aka yi a shekarar 2015, a wancan lokacin babu wanda ya ce Yakowa bai yi daidai ba.

Haka kuma wannan shugaban cocin  ya yi zargin cewa wai an kashe basaraken  nan Agwam Adara ne saboda yana gwagwarmayar ganin ba a mayar da masarautarsa karkashin masarautar Zazzau ba, shi ya sanya aka kama shi aka kashe bayan ya ziyarci gwamna el-Rufa’i lokacin da aka yi rikicin Kasuwar Magani da ke karkashin masarautar Adara din.

Sai dai kuma shi shugaban cocin bai yi bincike ba kafin ya yi wannan zargin, domin kuwa gwamna Ahmad Muhammad Makarfi ne ya kirkiro masarautar Adara, inda aka fitar da ita daga masarautar Zazzau, kafin wannan lokacin wannan yankin yana karkashin hakimin masarautar Zazzau ne . Kuma masarautar Adara ba ta hada iyaka da masarautar Zazzau ba, akwai masarautar Gbagyi a tsakaninsu, domin haka masaraurar Gbagyi ne yakamata a ce tana tsaron masarautar Zazzau za ta iya hadiye ta amma ba masarautar Adara ba.

Haka za ka ga irin wadannan limaman suna ta kirkiro karya suna fada wa mabiyansu domin tunzura su tare da cusa masu kiyayyar abokan zamansu.

Saboda haka ne har mataimakin gwamnan jihar Kaduna Akitek Barnabas Bala Banted a wannan karon ya fitar da wata sanarwa a nadadin kiristocin da ke aiki a gwamnatin jihar Kaduna, inda ya nesanta kansu daga irin wannan katobarar da limaman cocin suke yi, tare da nuna cewa a matsayinsa na mataimakin gwamna shi wakili ne a majalisar tsaro, domin haka duk shawarar da aka yanke da saninsa kuma babu wani matakin da aka  taba dauka da nufin musguna wa wadansu ko dadada wa wadansu duk abin da aka yi an yi ne domin amfanin jihar Kaduna baki daya.

Wannan ya nuna cewa ana zaton wuta a makera sai aka same ta a masaka, ana tunanin shugabannin addini ne za su rika kwantar da fitina amma sai ya kasance su ne kan gaba wajen rura wutar fitina, wanda ya sanya ake tababar anya irin wadannan limanan addinin sun fahimci addini kuwa?

Ya kamata irin wadannan mutanen su fahimci cewa babu wanda fitina take yi wa amfani, kuma an san farkon fitina ne amma ba a san karshenta ba, tana kuma iya lakume su wadanda suka tayar da ita.