✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Angela Merkel na gab da rasa mulkin Jamus

Sakamakon sauyin shugabanci da aka samu a kungiyar ’Yan Majalisar Dokoki na Jam’iyyar CDU ta Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, Shugabar tana gab da rasa…

Sakamakon sauyin shugabanci da aka samu a kungiyar ’Yan Majalisar Dokoki na Jam’iyyar CDU ta Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, Shugabar tana gab da rasa karfin fada-a-ji a jam’iyyar.

A tsarin siyasar Jamus, irin wadanan kungiyoyi ne ke wucewa gaba wajen ganin sun sama wa shugabansu rinjaye a cikin kungiyar, sannan idan ya kasance su ne ke rike da madafun iko to sukan taimaka wajen ganin shugaba ya yi aikinsa ba tare da fuskantar kalubale ba.

Sai dai duk da wannan a iya cewar lamura sun cije a gwamnatin Jamus musamman idan aka dubi abin ta fuskar tsawon lokacin da aka dauka kafin a kafa gwamnatin hadaka da yadda wadansu suka rika ajiye aiki da kuma barazanar da ake ci gaba da fuskanta da ka iya kaiwa ga rushe gwamnati da yin sabon zabe. Yanzu haka an kusa cika shekara guda bayan kafa gwamnatin, kuma akwai alamun  rushe gwamnati mai ci wanda hakan zai haifar da fafutikar kafa sabuwar gwamnati a kasar.

Angela Merkel ta rasa gagarumin goyon bayan da take da shi a tsakanin ’yan jam’iyyarta a Majalisar Dokoki ta Bundestag, domin sauke shugaban kungiyarsu kuma na hannun damanta, bolker Kauder daga matsayinsa abu ne da za a iya dangantawa da juyin mulki na cikin gida. Domin kuwa mambobin jam’iyyar Merkel ta CDU da abokiyar kawancenta ta CSU sun yi mata babbar illa baya ga kawar da Kauder a shugabancin  wakilan majalisar dokoki na CDU.

Hakan zai iya kaiwa ga yanayin da za a gudanar da sabon zabe ba tare da Merkel ba, wacce ake kallo a matsayin wadda ta kawo sauye-sauye a Jamus da Turai a tsawon shekara 13 da ta yi kan madafun iko.

Zaben da aka yi wa masanin tattalin arziki Ralph Brinkhaus a mastayin shugaban  kungiyar ’yan majalisa na Jam’iyyar CDU a daidai lokacin da Shugaba Donald Trump na Amurka ya caccaki Jamus a jawabinsa a Babban Taron Majalisar dinkin Duniya ya sanya da dama sake yi wa Jamus kallo na daban.