✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ango ya yi alwashin ba zai kara murna ba a rayuwarsa

Wani ango da ya hadu da tashin bam a yayin bikinsa a birnin Kabul na Afghanistan ya ce ba ya da sauran kwarin gwiwa bayan…

Wani ango da ya hadu da tashin bam a yayin bikinsa a birnin Kabul na Afghanistan ya ce ba ya da sauran kwarin gwiwa bayan mummunan harin.

A wata hira ta gidan talabijin, Mirwais Elmi ya  ce amaryarsa ta tsira amma sauran ’yan uwansa na cikin mutum 63 da suka rasa rayukansu a harin da aka kai ranar Asabar lokacin bikinsa.

A cikin hirar da ya yi da Tolo News, Mirwais Elmi ya ce ya tuna yadda ya rika gaisawa da bakin da suka cika dakin taron bikin nasa makil cikin annashuwa, amma kwatsam bayan ’yan sa’o’i sai aka rika fitar da gawarwakinsu.

“Amaryata da ’yan uwana duk suna cikin dimuwa, ba za su iya magana ba ma. Amaryar tawa ma sai suma take yi,” inji shi.

Ya ce “Ba ni da sauran kwarin gwiwa. Na rasa kanena, na rasa abokaina. Ba zan taba samun farin ciki a rayuwata ba.”

Ya kara da cewa: “Ba zan iya halartar jana’izarsu ba, ba ni da karfin zuwa. Na dai san wannan ba shi ne karo na karshe da mutanen Afghanistan za su sha wuya ba, za a ci gaba da shan wahala.”

Mahaifin amaryar ya bayyana wa kafafen watsa labarai na Afghanistan cewa ’yan uwansa 14 ne suka rasa rayukansu a yayin harin.