✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Annobar COVID-19: Yadda Musulmi zai ribaci 10 ta karshen Ramadan

Musulmi za su iya cin ribar kwanaki goma na karshen watan Ramadan duk da yanayin da ake ciki na zaman fargaba da dokar hana fita…

Musulmi za su iya cin ribar kwanaki goma na karshen watan Ramadan duk da yanayin da ake ciki na zaman fargaba da dokar hana fita a wasu wurare sakamakon mamayar annobar coronavirus.

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Almannar a Kaduna Shaikh (Dokta) Tukur Adam Al-Mannar ne ya fadi haka, ya kuma nemi Musulmi su dage da abdu’a da neman Allah Ya kawo karshen annobar a cikin goman na karshen watan Azumin Ramadan.

A wata tattaunawa da Aminiya a Kaduna, malamin ya ce kwanaki goma na karshe hukunce hukuncensu sun bambanta da goman farko da goma na biyu a watan, saboda a cikin wadannan kwanakin ne ake laluben dare mai albarka watau daren Lailatul Kadri.

Ya ce Nana Aisha Allah shi yarda da ita ta ce Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi ya kasance a goman karshe yakan zage damtse kuma yana tashin iyalansa domin sallatar daren wadannan kwanaki.

Raya dare

“Ya kan rayar da kwanakin baki daya ba ya barci ta hanyar yin tahajjud da kuma istigifari da azkar da ambaton Allah.

“Kokarin da Manzon Allah ke yi a wadannan lokutan wato goman karshe gaskiya daban ne da kwanakin Ramadana da ba su ba.

“Manzon Allah yakan ziyarci masallaci da sunan itikafi. Kamar yadda aka saba kuma a masallatai ake yi amma sai ga wata lalura ta fado mana na babu halin a je masallatan.

“To malamai sun ba da fatawa cewa mutum zai iya yin itikafinsa a gida saboda malamai sun yi sabani – wadansu suna ganin cewa itikafi ba ya yiwuwa sai a masallaci wadansu kuma na cewa masallaci shi ne wajen sallarka.

“Nan ne kake lizimta wajen salla. To yanzu tun da gidanka kake lizimta wajen sallar sai gidan ya maye maka gurbin masallaci.

“Mutum sai ya yi itikafinsa a nan ya bauta wa Allah gwargwadon yadda ya samu, saboda mata suna yin itikafi a gida a zamanin Manzon Allah.

“Nan ne wajen sallarsu da shariah ta ajiye su sai ya zamanto wajen sallarsu nan ne wajen itikafinsu.

“Kai ma yanzu tun da an lizimta maka zama gidan da ma wajen sallarka shi ne masallaci yanzu an mayar da shi a bisa lalura zuwa gida kaima sai hukuncin wajen sallarka ya zamanto maka shi ne wajen itikafinka.

“Wannan a ra’ayin wadansu malamai ke nan; saboda haka Musulmai su yi kokari kwarai da gaske su zage damtse wajen ibada da tahajjud – sallolin dare – da zage damtse wajen yawaita addu’o’i da kokarin dacewa da daren lailatul kadri”, inji malamin.

A yanayin annoba

Shaikh Tukur ya kuma yi kira ga Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci don komawa ga Allah da fatan zai yaye dukkan bala’i.

“Musamman a wannan yanayi da muke ciki na wannan annoba da ba a san karshensa ba sai wanda Ya jarrabe mu da ita Shi ne Allah a roke Shi afuwa a roke Shi gafara a roke Shi yafiya a dawo maSa a sunkuyar da kai.

“Manzon Allah Nana Aisha ta tambaye shi ya rasulalLah wacce addu’a ce ta fi da musulmi zai rika yi a goman karshe?

“Sai Annabi ya ce mata Allahumma innaKa Afuwwun, tuhibbul afwa ‎fa’afu anna. Lallai ya Allah Kai mai afuwa ne kuma kana san afuwa. Ya Allah Ka mana afuwa.

“Aka ce neman afuwa ya fi neman gafara – bambancin gafara da afuwa shi ne gafara mutum ya yi laifi amma ga laifin a cikin fayil dinsa an ce ba za a nuna ba an yafe masa. Amma ba ba za a nunawa kowa ba.

“Amma ita kuma afuwa ita ce bayan mutum ya yi laifi an kuma yafe maka a dauki wannan takarda a fayil dinka a kona.

“Ka ga baki daya wannan ya fi karfi. To shi ya sa Manzon Allah ya ce a rika ba da himma wajen fadin Allahumma innaKa Afuwun tuhibbul afwa fa’afu anna.

A roki Allah sosai

“A roki Allah sosai a kan wannan bala’i na coronavirus Allah Ubangiji Ya kawar mana da shi sannan Allah Ya sa alkhairi mai dimbin yawa ya biyo baya.

“Alhairin kasuwannin da aka rufe ya zamanto bayan coronavirus kasuwanni su yi albarka su ninka riba su habaka su yi albarka sama da yadda suke kafin cutar.

“Da kuma tattalin arzikinmu na Najeriya da kuma ma’aikatun gwamnati dukka da aka rufe su kudi ba su shigowa, arziki ba ya shigowa. to Allah Ya ninninka arzikin bayan wucewar cutar.

“Allah Ya ninka wa mutane lafiya bayan COVID-19, Ya ninka masu imani da tuba zuwa ga Allah bayan jarabawar mace-mace da aka gani.

“Sannan wadanda suka kamu suka warke sun san irin radadi da zafin da suka sha Allah Ya sa abin ya zamanto‎ komawa ga Allah gaba daya ne har mutuwa.

“Wuraren fasadi da fasikanci da aka kulle su kuma Allah Ya sa an kulle su na har abada ke nan.

“Abinda za a yi ta roka ke nan sannan a rokan ma shugabanni da suka yi ta kokari wajen ganin sun yaki cutar nan da kuma zargin da ake masu wai neman kudi ne ba a yarda ba.

“A kuma jinjina wa likitocinmu masu albarka da suka hango wannan bala’i da yake fanninsu suka fadakar da al’umma cewa ga yadda za a kauce masa – wadansu ma sun rasa rayukansu, wasu kuma sun bar iyalansu saboda kokarin ceto rayuka.

An zargi malamai

“Haka nan malamai ma ba za a bar su ba duk da cewa an sha zagi da tuhume tuhume ga malamai cewa an saye su.

“Amma masu kyakkyawar manufa sun san manufar malaman – su ma a yi masu addu’a Allah Ya yi masu albarka.

“Wannan shi ne abin da za a dukufa da yi sannan kuma ‘yan jarida a saka ku cikin addu’a domin kuna yada alkhairi da abubuwan da ake yi a boye ku bayyana wa duniya; Allah Ya yi maku albarka Ya sa ku gama da duniya lafiya.” inji malamin.