Da Dumi Dumi

APC da Oshiomhole sun yaba wa karamcin  Jonathan

Jam’iyyar APC ta yaba da yadda tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya karbi zaben Jihar Bayelsa da aka yi a makon jiya. APC ta ce Jonathan ya ji dadin yadda zaben ya kasance duk da dan takarar Jam’iyyar APC Dabid Lyon ne ya yi nasara a kan dan takarar PDP, Diri Douye. Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Sanata Atiku Bagudu ne ya gabatar wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da zababben Gwamnan Bayelsa. Atiku Bagudu ya ce Mista Jonathan ya yi murna da yadda zaben ya gudana. Ya ce: “Kwananmu uku a Jihar Bayelsa, amma ba mu ga an kona da ko tayar mota ba. Ba mu ga mutane su na gudu ba, ba mu ji harbin bindiga a ko’ina ba. Duk inda muka wuce sai murna kawai ake ta faman yi, wannan ya nuna karbuwar  zababben Gwamnan,” inji Bagudu.

Gwamna Bagudu ya kara da cewa “Duk da Bayelsa Jihar tsohon Shugaban Kasa Jonathan ce, kuma wata jam’iyya ta daban ta karbe mulki, abin da muke gani shi ne ya amince da zaben.” Shugaban Gwamnonin Jam’iyyar APC din ya ce, abin da suke jin labari kuma suka gani a zahiri daga Jonathan shi ne ya karbi nasarar APC da hannu biyu wannan ya nuna sahihancin zaben jihar.

Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole wanda ya gabatar da zababben Gwamnan, ya ce wannan ne karon farko da aka yi zaben gaskiya a Bayelsa tun 1999. Oshomhole ya kuma yaba wa Mista Jonathan wanda ya ce ya nuna saukin kai da kirki da jajircewa wajen karbar jagororin APC. Sannan Oshiomhole ya gode kan kokarin da Minista a Ma’aikatar Man fetur Timipreye Sylba ya yi.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya