✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC da PDP suna kankankan a Majalisar Wakilai

Jam’iyyar APC ta rasa rinjayen da ta samu a Majalisar Wakilai ta Tarayya a watan jiya, inda a ranar Talatar da ta gabata suka yi…

Jam’iyyar APC ta rasa rinjayen da ta samu a Majalisar Wakilai ta Tarayya a watan jiya, inda a ranar Talatar da ta gabata suka yi kankankan da Jam’iyyar PDP bayan da wani dan majalisar daga Jihar Nasarawa ya sauya sheka zuwa PDP. A yanzu APC da PDP suna da wakilai 173 kowaccensu.
dan majalisa Joseph Haruna Kigbu na APC daga Jihar Nasarawa ya koma PDP ne bayan mako biyu da takwarorinsa daga Adamawa suka yi haka.
Lokacin da wakilai 37 suka bar PDP zuwa APC a ranar 18 ga Disamban bara, APC ta samu rinjaye da wakilai 174, yayin da PDP ked a 171, sai dai an rika samun sauyin yawan wakilan yayin da aka dawo hutu a Talatar makon jiya, inda a ranar sauya shekar wakilai biyu Titsi Ganama da Haske Hananiya daga Adamawa zuwa PDP ya sa ta gusa daf da APC. Sai dai canja shekar da Emmanuel Jime na PDP daga Benuwai da Yahya Kwande na DPP daga Filato zuwa APC ya sa ta ci gaba da rinjaye da wakilai 174 PDP 172.
Kigbu ya ce ya bar APC ne saboda narkewar jam’iyyarsa ta CPC a cikin APC, lamarin da bai gamshe shi ba. Da wannan sauyin sheka ne ya sa APC da PDP suka yi kankankan da wakilai 173 kowaccensu.
Saura kujeru 14 jam’iyyun APGA da Accord da LP da DPP ne suke da su, kuma galibi idan aka zo yanke shawara kan muhimman al’amura sukan goya wa PDP baya ne. Wakilanmu sun ce ko a ranar sun gan su tare da Shugabar Masu Rinjaye Mulikat Adeola Akande a karkshin wata sabuwar kungiya mai suna Unity Group, inda suka yanke shawarar yakar APC, idan wakilanta suka yi yunkurin sanya birki ga amincewa da kasafin bana kamar yadda jam’iyyarsu ta nema.
Wannan lamari na iya sauya tunanin karbe shugabancin majalisarda APC ke niyyar yi da sunan rinjayenta a majalisar.