✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…APC ta dakatar da Oshiomhole

Bangaren Jam’iyyarr APC a Jihar Edo ta sanar da dakatar da Shugaban Jam’iyyar ta Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, bisa zarginsa da hannu a rikicin da…

Bangaren Jam’iyyarr APC a Jihar Edo ta sanar da dakatar da Shugaban Jam’iyyar ta Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, bisa zarginsa da hannu a rikicin da APC ke fama da shi a jihar. Jam’iyyar ta dakatar da Oshiomhole ne bayan kada kuri’ar rashin amincewa da shi da shugabannin Jam’iyyar APC a kananan hukumomi 18 na jihar suka yi.

A wani jawabi da Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Edo, Anselm Ojezua da Mataimakin Sakataren Jam’iyyar, Ikuenobe Anthony suka fitar, sun ce, “Shugabannin Jam’iyyar sun zauna domin duba halin da APC ke ciki a jihar, kuma sun nuna rashin amincewa da shi, lamarin da ya sa suka kada kuri’a tare da amincewa da dakatar da shi daga jam’iyyar a matakin jiha.”

’Ya’yan jam’iyyar sun kara da cewa, daukar matakin ya zama dole, domin kiyaye faruwar abin da ya faru a jihar Zamfara. inda APC ta shiga zabe ba tare da fid da ’yan takara ba. “Adams Oshiomhole ne tushen duk rikicin da APC ke fama da shi a Jihar Edo. Mun kada kuri’ar nuna rashin amincewarmu da shi. Ba ma son abin da ya faru a Jihar Zamfara da sauran sassan Najeriya ya maimaita kansa a Jihar Edo,” inji sanarwar.