✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta doke PDP a zaben Nasarawa ta Tsakiya

Dan takarar jam’iyyar APC mai mulki, Ismail Danbaba ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar adawa ta PDP, Iliyasu Umar, a zaben maye gurbin Mazabar Nasarawa…

Dan takarar jam’iyyar APC mai mulki, Ismail Danbaba ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar adawa ta PDP, Iliyasu Umar, a zaben maye gurbin Mazabar Nasarawa ta Tsakiya.

An yi zaben ne domin maye gurbin dan majalissar dokoki, Suleiman Adamu, da COVID-19 ta yi sanadiyyar rasuwarsa a watan Mayu.

An gudanar da zaben karkashin sa idon Kwamishinan Zabe na Tarayya mai kula da Jihohin Kogi da Nasarawa da Kwara, Malam Mohammed Haruna, a cikin tsauraran tsaro.

Da yake bayyana sakamakon zaben, baturen zaben na Hukumar Zabe ta Kasa, (INEC) Iliyasu Umar, ya ce dan takarar APC ya samu kuri’a 7,475 kuma ya doke dan takarar PDP da ya samu kuri’a 4,608.

Iliyasu ya ce, an jefa adadin kuri’u 12,217 wadanda 12,083 ne masu kyau, aka kuma yi asarar 234.