✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta hana ministoci biyu takarar Gwamna

Jam’iyyar APC ta fitar da jerin sunayen mutanen da ta tantance masu son tsayawa takarar gwamna a jihohin Najeriya 29, sai dai ba ta tantace…

Jam’iyyar APC ta fitar da jerin sunayen mutanen da ta tantance masu son tsayawa takarar gwamna a jihohin Najeriya 29, sai dai ba ta tantace wasu ministocin gwamnati mai ci biyu da ke son tsayawa takarar gwamna ba.

Ministocin dai sun hada da Barista Adebayo Shittu na ma’aikatar sadarwa wanda ke takarar gwamnan jihar Oyo da kuma Aisha Jummai Alhassan ministar mata, wacce ke neman takarar gwamnan jihar Taraba.

Jam’iyyar APC ta sanar cewa, ba ta tantance Barista Adebayo daga cikin ‘yan takarar gwamna takwas na jihar ba, saboda rashin shaidar yi wa kasa hidima NYSC da ba shi da ita. Yayin da sanarwar ba ta bayyana dalilin da ya sa ba a tantance Aisha Jummai Alhassan a matsayin ‘yar takarar gwamnan Taraba ba daga cikin mutum 12 da suke takarar.

Sauran wadanda jam’iyyar ba ta tantance ba sun hada da: Ibrahim Mohammed Mera wanda ke neman kujerar Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi da Danladi Halilu daga jihar Nasarawa da Abubakar Mamma Ma’aji daga jihar Neja da Barista Ejikeme Ugwu daga jihar Enugu.

Ibrahim Bomai ya janye neman takarar na jihar Yobe.

Da farko an dai shirya zaben fidda gwanin ne a ranar Asabar 29 ga Satumba 2018 daga bisani aka mayar zuwa ranar Lahadi 30 ga Satumaba kamar yadda muddashshiyar sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa Yekini Nabena ta sanar.