Da Dumi Dumi

APC ta hana ’ya’yanta magana kan binciken da ake yi wa Yari

Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Zamfara Alhaji Lawal Liman ya gargadi ’ya’yan jam’iyyar da kada su saka baki a kan binciken da ake yi wa tsohon Gwamna Jihar Abdul’aziz Yari Abubakar.

Hukumomin EFCC da ICPC suna bincikar tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari kan zargin wawurar kudin jihar lokacin  da yake Gwamnan Jihar Zamfara.

Alhaji Liman ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar na jihar su kame bakinsu daga cewa komai game da wannan bincike har sai an kammala.

Ya ce Alhaji Abdul’aziz Yari mutum ne mai bin doka da oda saboda haka yana kiran ’ya’yan jam’iyyar da su ci gaba da bin dokokin jam’iyyar su guji yin maganganu a kan wannan batu.

ADVERTISEMENT
Share