✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta kaddamar da kamfen a Kudancin Kaduna

A ranar Alhamis din makon jiya ne wadansu fitattun ’ya’yan Jam’iyyar PDP a Kudancin Kaduna suka sauya sheka zuwa APC a wani gangami da jam’iyyar ta…

A ranar Alhamis din makon jiya ne wadansu fitattun ’ya’yan Jam’iyyar PDP a Kudancin Kaduna suka sauya sheka zuwa APC a wani gangami da jam’iyyar ta gudanar a filin wasa na garin Kafanchan don kaddamar da kamfen dinta a shiyyar.

Taron wanda ya samu halartar wadansu kusoshin jam’iyyar da suka hada da Shugaban Jam’iyyar APC ta Jihar Kaduna wanda  dan yankin ne, Kwamared Emmanuel Jekada  da Mataimakiyar ’yar takarar Gwamna Dokta Hadiza Sabuwa Balarabe da shugabannin jam’iyyar na yankin.

Da yake gabatar da jawabi, Shugaban APC a Jihar Kaduna, Emmanuel Jekada ya bayyana APC a matsayin jam’iyyar da ta kawo ci gaba a jihar tare da gudanar da muhimman ayyuka da suka hada da gyaran hanyoyi da makarantu da asibitoci.

Sai ya bukaci jama’ar yankin Kudancin Kaduna su daina ware kansu su zo su ji gwamnati don cin gajiyar mulkin dimokuradiyya.

Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban kamfen din Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i, Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna, Mista Ben Kure, ya bayyana sauya shekar da wadansu fitattun yankin suka yi a matsayin gagarumin ci gaba da nuna yadda mutanen yankin suka fara dawowa daga rakiyar siyasar kabilanci da wasu marasa son ci gaban yankin suka hurawa.

’Yar takarar Mataimakiyar Gwamnan, Hajiya Hadiza Abubakar Balarabe, janyo hankalin jama’ar yankin ta yi cewa su yi watsi da siyasar addini su yi abin da zai fisshe su.

Dakta Hadiza, ta ce kokarin da Gwamna El-Rufa’i ya yi da wanda yake kan yi na bai wa mata mukamai a cikin gwamnatinsa dalili ne da ya wajaba a ce mata sun antayo ruwan kuri’unsu wajen sake zabar Gwamna  El-Rufa’i da sauran ’yan takarar APC a dukan mukamai a zabe mai zuwa don samun riba da kuma romon dimokuradiyya.

Wadanda suka sauya shekar sun hada da Jarman Kauru da Honorabul Antokuze da Honorabul Musa Isa da Barista James Kanyip da sauransu. Mawaka da ’yan wasan gargajiya daga kabilu daban-daban ne suka burge mahalarta taron da irin bajintarsu.