✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta kama hanyar lashe zaben Gwamnan Osun

Jam’iyyar APC ce ta kama hanyar kafa gwamnati a Jihar Osun inda a daidai lokacin hada wannan rahoto a jiya Alhamis take kan gaba a…

Jam’iyyar APC ce ta kama hanyar kafa gwamnati a Jihar Osun inda a daidai lokacin hada wannan rahoto a jiya Alhamis take kan gaba a zaben da aka fafata tsakaninta da PDP wadda ta wuce ta da kuri’a 356, a zaben Asabar da ta gabata.

Duk da cewa lokacin hada wannan rahoto babu jam’iyyar da Hukumar INEC ta  bayyana cewa ta yi nasara a zaben da jam’iyyun biyu suka lashi takobin lashe shi amincewar dan takarar SDP, Iyiola Omisore da ya zo na uku a zaben na mar awa APC baya don samun nasara a karashen zaben ya sa jam’iyyar ta rika samun nasara a sauran rumfunan da aka yin zaben.

Daga farko an rika samun rahotannin cewa an hana masu zabe da ’yan jarida da masu sa ido a zabe zuwa rumfunan zabe. Amma Hukumar INEC, ta shelanta cewa an warware matsalolin da aka samu. Ta kuma kara da cewa zaben na ci gaba, duk da cewa ana ruwa kamar da bakin kwarya a wasu wuraren. Haka Rundunar  ’Yan sanda da ke aikin ba da kariya a zaben Gwamnan Jihar ta ce ta kama wadansu mutum 16 da kayan zabe na jabu a daidai lokacin da ake kada kuri’un a jiya Alhamis.

Sanarwar da Kakakin Hukumar ’Yan sandan, Folasade Odoro ta fitar, ta ce an kama mutanen ne da kayayyakin masu sa ido a zabe na jabu da kuma katin zama dan Jam’iyyar PDP.

Mutanen da aka kama din sun hada da Moshood Adejare da ke neman takarar kujerar dan Majalisar Wakilai a mazabar Orolu a karkashin PDP da Oyelayo Dayo, dan PDP daga karamar Hukumar Orolu da Olaoye Asimi, dan PDP daga karamar Hukumar Orolu da kuma Raimi Taofeek Sakataren PDP na karamar Hukumar Orolu.