Da Dumi Dumi

APC ta kwace wa PDP rinjaye a Majalisar Tarayya • Komawar ’yan majalisa APC, butulci na ga ’yan Najeriya – PDP

Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan ta rasa rinjayenta a Majalisar Tarayya, sakamakon canja sheka da ’yan majalisar 37 suka yi, lamarin da ya kawo sabon shafi a Majalisar Dokoki a karo na farko tun 1999.
Wakilan 37 da suka koma APC sun fito ne daga jihohin Kano da Sakkwato da Bauchi da Kwara da Ribas da Katsina da kuma Adamawa.
A wata wasikar hadin gwiwa da Shugaban Majalisar Tarayya Aminu Tambuwal ya gabatar a zaman majalisar, masu canja shekar sun ce sun fice ne daga PDP sakamakon hadewar bangarensu da APC.
Hakan ya sa APC ta zamo jam’iyya mafi yawan ’yan majalisar tarayya a majalisar mai wakilai 360, inda take da wakilai 174 daga wakilai 137 da take da su a farko, yayin da PDP take da wakilai 171, inda ta yi kasa daga wakilanta 208.
Sauran wakilan majalisar sun fito ne daga jam’iyyun Labour mai wakilai 10, sai APGA mai wakilai biyar Jam’iyyar Accord hudu sai DPP mai daya.
Sai dai PDP ta ci gaba da kasancewa mafi rinjaye a Majalisar Dattawa zuwa shekaranjiya Laraba, sai dai akwa sanatoci kimanin 20 da suke ganawa domin yanke shawara kan bayyana canjin shekarsu, lamarin da zai kawo sauyin iko a majalisar.
Canjin shekar ta shekaranjiya ta zo ne bayan makonni da gwamnonin jihohin Kano da Adamawa da Sakkwato da Kwara da Ribas suka bar PDP zuwa APC, sakamakon shafe watanni ana rikici kan shugabancin jam’iyyar.
Sabon fasalin iko a majalisar dokokin wata barazana ce ga shugabancin majalisar da a yanzu wakilan PDP ke rike da shi.
Akwai yiwuwar a maye gurbin manyan shugabannin majalisar da suka fito daga PDP, amma ana sa ran Tambuwal zai ci gaba da rike kujerarsa saboda tun farko ya samu nasarar zama shugaban ne da gagarumar goyon bayan da ’yan adawa.
Majiyoyin majalisar sun ce ana jin shi ma zai fice daga jam’iyyar a Janairu mai zuwa, ganin cewa tuni gwamnansa da sauran abokansa ’yan majalisa sun fice daga jam’iyyar.
Da yake tattaunawa da Aminiya dan Majalisar Tarayya Mustapha Bala Dawaki daga Jihar Kano ya ce, “Mu ne rukuni na farko na wadanda suka koma APC, nan da Janairu wasu wakilan za su biyo mu.”
Game da ko za su cire shugabannin majalisar, Dawaki ya ce, “Ba mu son mu yi wannan a yanzu. Ba za mu taba shugabannin majalisar yanzu ba.
 
‘Rarrabuwa da bangarewa’
Da safiyyar shakranjiya ce aka sanar da ficewar ’yan majalisar ta wata wasika da suka sanya mata hannu. Wasikar mai kwanan wata 18 ga Disamba mai taken: “Sanar da canja jam’iyyar siyyasa,” sun ce, “Mu wadannan wakilan Majalisar Tarayya a karkashin Jam’iyyar PDP, muna son sanar da ku cewa mun koma Jam’iyyar APC. Mun yi haka ne sakamakon rarrabuwa da bangarewar da ke cikin jam’iyyar da aka zabe mu a karkashinta. Sakamakon wannan rarrabuwa bangaren PDP da muke ciki ya hade da APC. Wannan sanarwa mun yi ne kamar yadda sashi na 68 (1) (g) na Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 domin sanar da ku da kuma adanawa.”
Tambuwal na kammala karantar wasikar sai zauren majalisar ya kaure da tafi da ihu, wasu suna cewa sai “APC!”
Wakilan 37 a karkashin jagorancin shugaban masara rinjaye sun yi layi sahu zuwa gaban shugaban majalisar domin gabatar da kansu.  Suna daga hannuwa domin murna, yayin da sauran wakilan PDP suka yi zugum suna kallo.
A daidai da lokacin da haka ke gudana, sai Kingsley Chinda (PDP, Ribas) da Patrick Asadu suka gabatar da sanarwar wata shari’a da ke gaban kotu da ta ce kada a amince da canjin shekar.
Tambuwal ya ce ya samu umarnin kotun ne da ke hani kan yin amfani da tanadin tsarin mulki game da batun canja shekar da safiyar ranar. Sai ya ce zai nazarci batun tare da sanar da majalisar.
 
karin masu canja sheka
Wani dan majalisar ya shaida wa Aminya cewa Tambuwal zai koma APC tare da kashi na karshe na ’yan majalisar a watan Janairu mai zuwa lokacin da Majalisar Tarayya ta dawo daga hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.
Ya ce shugaban majalisar zai ‘sauka daga mukaminsa na wasu awanni a nada shugaba na takaitaccen lokaci kafin komawarsa APC ya kammala.’
daya daga cikin wakilan PDP da suka saura Ibrahim Tukur El-Sudi (PDP, Taraba), ya ce bai yanke kaunar ficewa daga PDP ba, matukar ta gaza daidaita al’amuranta.
Aminiya ta samu bayanin cewa wasu manyan wakilan APC da PDP a majalisar sun yi taro da shugabannin APC a ranar Larabar makon jiya inda aka kammala shirye-shiryen canjin shekarsu.
An gudanar da taron ne a masaukin baki na Gwamnan Kano da ke Abuja, kuma cikin wadanda suka halarci zaman akwai Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da shugaban riko na Jam’iyyar APC na kasa Cif Bisi Akande da sanatocin da suka hada da Abdullahi Adamu da Abubakar Bukola Saraki da danjuma Goje da Ahmed Lawan da Umaru dahiru da George Akume da kuma A’isha Jummai Alhassan.
Kotu ta tsare kujerunsu
Babbar Kotun Tarayya ta Abuja a ranar Talata ta ba da odar da ke hana Shugaban Majalisar Dattawa Dabid Mark da na Tarayya Tambuwal da Hukumar Zabe ta kasa (INEC) da shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Bamanga Tukur daga bayyana raba sanatoci 22 da wakilan Majalisar Tarayya 57 da suke bangaren PDP ta Kawu Baraje da kujerunsu.
Kwafin umarnin da Aminiya ta ci karo da shi ya nuna cewa Mai shari’a A. R. Mohammed ya ba da odar kowa ya tsaya game da yanke shawara kan bayyana raba masu kujerun da kujerunsu a tsakanin bangarorin da ke takaddama, akalla har zuwa lokacin da kotun za ta saurara tare da yanke hukunci kan karar da ke gabanta game da batun.
Sanatoci 22 da wakilai 57 ne suka shigar da karar a ranar 28 ga Nuwamba, kuma an dage sauraron karar zuwa 22 ga Janairu mai zuwa.
Kwamitin Gudanarwa na kasa (NWC) na Jam’iyyar PDP ya bayyana ficewar wakilan majalisar 37 daga jam’iyyar zuwa APC a matsayin butulci ga jam’iyyar da ’yan Najeriya.
Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar na kasa, Olisa Metuh ya ce bayan cikakken nazarin rahoton canja shekar a hedkwatar jam’iyyar ta kasa ta ce lura da hukuncin kotu PDP, ba ta rarrabuwa ko rikicin cikin gida a cikinta.
“A matsayinsu na masu kafa dokoki, masu canjin shekar ba shakka suna sane da tanade-tanaden sashi na 68 (1) (g) na tsarin mulkin Najeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara) wanda ya bayyana balo-balo dalilin da dan majalisa zai canja sheka.”

 

Wakilai 37 da suka koma APC daga PDP

Jihar Kano:
1.  Nasiru Sule Garo
2. Ahmad A. Zarewa
3.Aliyu Sani Madaki
4. Bashir Baballe
5. Alhassan Ado Doguwa
6. Mannir Babba dan-Agundi
7.Aminu Suleiman Goro
8. Abdulmumin Jibrin
9. Musa Ado Gezawa
10. Mustapha Bala Dawaki
11. Mukhtar I. Mohammed Ciromawa
Farouk Lawan da Muhammad Bashir Galadanci har yanzu
 suna PDP.

ADVERTISEMENT

Jihar Sakkwato:
1. Kabiru Marafa Achida
2. Aminu Shagari
3. Isa Salihu Bashir
4. Abdullahi Mohmmed Wammako
5. Sa’adu Nabunkari
6. Aliyu Shehu
7. Shu’aibu Gobir
8. Musa Sarkin Adar
9. Dokta Abdullahi Balarabe Salake
10. Umar M. Bature

Jihar Ribas:
1. Andrew Uchendu
2. Asita Honourable
3. Sokonte Dabies
4. Dakuku Peterside
5. Mpigi Barinada
6. Pronen Maurice
7. Dawari George
8. Ogbonna Nwuke

Jihar Kwara:
1.Ali Ahmad
2. Rafi’u Ibrahim
3.Aiyedun Akeem
4. Mustapha Mashood
5. Aliyu Ahman Patigi
6. Zakari Mohammed

Jihar Bauchi:
1. Yakubu Dogara

Jihar Katsina:
1. Nasiru Sani Zangon Daura

Share