Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

APC ta lashe zaben cike-gurbi na dan Majalisar Dokokin Jihar Filato

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Yakubu Sanda na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben cike-gurbi, na dan Majalisar Dokokin Jihar Filato a Mazabar Pengana, da ke Karamar Hukumar Bassa da aka gudanar, a ranar Asabar da ta gabata.

Zaben cike-gurbi an gudanar da shi ne, sakamakon rasuwar dan majalisar mazabar, Mista Ezekiel Afon Bauda, wanda ya rasu a lokacin da ake tsakiyar bikin murnar cin zabensa karo na biyu a gidansa da ke garin Jos a zaben da ya gabata.

ADVERTISEMENT

Da yake bayyana sakamakon zaben a cibiyar tattara sakamakon zaben da ke Kwalejin Gwamnati a garin Jingir, babban jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Noel Wanang ya ce an gudanar da zaben ne, a rumfun 127 da ke mazabu 7 na mazabar ta Pengana.

Ya ce a zaben da aka fafata, Yakubu Sanda na Jam’iyyar APC ya samu kuri’a 9,222, yayin da Yakubu Busa Buji na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 7, 083. Don haka ya bayyana Yakubu Sanda na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

ADVERTISEMENT

Da yake zantawa da wakilinmu bayan bayyana sakamakon zaben, zababben dan majalisar Yakubu Sanda, ya nuna matukar farin cikinsa kan yadda al’ummar mazabarsa, kan yadda suka fito suka zabe shi.

Ya yaba wa al’ummar mazabar kan yadda aka gudanar da zaben lafiya ba tare da wata hayaniya ba, inda ya ba da tabbacin cewa zai yi iyakar kokarinsa wajen ganin gwamnati ta share wa al’ummar mazabar koke-kokensu.

Ya yi kira ga wanda suka yi takara tare da ya ba shi goyon baya da hadin kai, domin ganin an ciyar da Mazabar Pengana da  Karamar Hukumar Bassa da Jihar Filato gaba.