✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta lashe zaben duk Kananan Hukumomi 21 na jihar Kebbi

Hukumar zabe ta jihar Kebbi (KESIEC), ta sanar da sakamakon zaben Kananan Hukumomin jihar da aka yi ranar a 26 ga watan Oktoba 2019 yayin…

Hukumar zabe ta jihar Kebbi (KESIEC), ta sanar da sakamakon zaben Kananan Hukumomin jihar da aka yi ranar a 26 ga watan Oktoba 2019 yayin da jam’iyyar APC tayi nasarar lashe zaben a dukkanin Kananan Hukumomin jihar, kamar yadda shugaban hukumar zaben Jihar Alhaji Aliyu Mera, ya sanarwa manema labarai yau Alhamis.

“Jam’iyyar APC ita ce tayi nasarar lashe zabukan da aka gudanar a dukkanin kanan hukumomi 21 na jihar. Jam’iyyun PDP da FP da sauran abokan karawa basu yi wani abin azo a gani ba a zaben.” in ji shi.

Ya kara da cewa, an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali ba tare da hatsaniya ba, kuma an bayyana sakamakon a gaban wakilan kowace jam’iyya.