Da Dumi Dumi

APC ta lashe zaben Gwamnan Osun

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC ta sanar da cewa Gboyega Oyetola dan takarar gwamna a jam’iyyar APC shi ne ya lashe zaben gwamnan Osun.

Gboyega Oyetola ya doke Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP da kuri’u 482 bayan da a baya ya sami kuri’u 255,505, inda shi kuma Adeleken ya sami kuri’u 255,023 bayan zabe zagaye na biyu da ya gudana a jiya Alhamis.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Osun Olasoji Adagunodo ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar ta INEC ta sanar.

ADVERTISEMENT
Share