Da Dumi Dumi

APC ta rasa kujerun ’yan Majalisar Wakilai a Sakkwato

Kotun Daukaka Kara ta soke zaben dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Sakkwato ta Kudu da ta Arewa, Alhaji Hassan Bala Abubakar (Durumbun Sakkwato) na Jam’iyyar APC.

Alkalin Kotun Mai shari’a Frederick Oho ya umarci Hukumar INEC ta sanya ranar sake zabe cikin kwana 90 daga lokacin da aka yanke hukuncin.

Dan takararar Jam’iyyar PDP Abubakar Abdullahi (Abu Audu) ne ya kalubalancin nasarar da dan majalisar ya samu a kotun kararrakin zabe, inda aka yi watsi da karar tasa, hakan ya sa ya daukaka kara inda aka soke zaben.

Mazabu uku ne za a sake zabe a rumfuna 200, kuma jam’iyyun biyu APC da PDP suna iya taka rawa don samun nasara a zaben.

Haka Kotun Daukaka Karar ta soke zaben Sanata Abubakar Shehu Tambuwal  mai wakiltar Sakkwato ta Kudu da  dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan hukumomin  Bodinga, Dange Shuni da Tureta, Alhaji A. Aliyu Shehu dukkansu na Jam’iyyar APC, inda kotun ta ba Sanata Ibrahim Danbaba Dambuwa da Shehu Balarabe Kakale na PDP kujerun.

ADVERTISEMENT

Dukkansu sun daukaka kara ce kan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke na watsi da korafinsu.

Da yake yanke hukuncin Mai shari’a Federich Oho ya ce ya gamsu da korafe-korafen da masu daukaka kara suka gabatar don haka su ke da gaskiya.

Jam’iyyar PDP a Sakkwato ta samu nasara a karo na biyu cikin kwana biyu da fara yanke hukuncin Kotun Daukaka Kara ta Sakkwato.

Share