Da Dumi Dumi

APC ta soki yadda gwamnatin Tambuwal ke tafiya

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal

Jam’iyyar APC a Jihar Sakkwato ta nemi sanin halin da kasafin kuɗin bara ya kwana a jihar ganin manyan ayyukan da ke cikin kasafin ba a yi su ba kuma ba wani labari kansu, abin da take ganin ko kasafin 2020 fada ne ba cikawa.

Shugaban Jam’iyyar APC ta Jihar Alhaji Isah Sadik Achida ya bayyana haka a wurin taron manema labarai da suka kira a hedikwatar jam’iyyar  da ke Sakkwato.

“Lokacin da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana a gaban Majalisar Dokoki domin gabatar da kasafin kudin da ya yi wa lakabi da: “Kasafin Kudi Don Ci Gaban Tattalin Arziki da Walwala” da kowa zai morewa  ya zo ya wuce kamar ruwan fako jama’ar Jihar Sakkwato sun san cewa ’yar gidan jiya ne an fada ne kawai, ba aikin za a yi ba, iyakar labarin gidajen watsa labarai da jaridu. A duk shekara haka ake yi,” inji Isah Sadik Achida lokacin da yake yi wa manema labarai bayani.

Ya ce Gwamna Tambuwal ya saba wa yadda ake yi a duniya ba jawo rufe da ya yi a kasafi ba, sai an fada wa majalisa da jama’a inda aka kwana da nasarori da matsaloli wadanda gwamnati ta fuskanta a yayin aiwatar da kasafin kudi mai wucewa.

Alhaji Achida ya kawo wasu muhimman ayyuka biyar da ya ce gwamnatin ta aminta za ta yi a bara amma ba a yi ba har yanzu, irin su gyaran filin jirgi da za a kashe Naira miliyan 548 da karin gine-gine a harabar dakin taro na kasa da kasa da ke Kasarawa kan Naira miliyan 128 da ginawa da samar da kayan aiki a Cibiyar Binciken Cututtuka a kan Naira biliyan biyu da samar da manyan littattafan karatu a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari kan Naira miliyan 96.7 da yin gyare-gyare a Kwalejin Sana’a da Kere-Kere da ke Bafarawa kan Naira miliyan 98.83

ADVERTISEMENT

Alhaji Isah Achida ya ce gwamnatin ta samu wani salon labewa ga kungiyoyi da hukumomin kasashen waje domin su gudanar mata da manyan ayyuka ita kuma ta kafa alama cewa ita ta yi.

“Wuraren zuba shara da ake bugun gaba an gina muna da tabbacin cewa Bankin Duniya ne ke ginawa a karkashin shirinsa mai suna ‘NEWMAP,’ haka yashe magudanun ruwan da aka yi su ne suka yi don haka gwamnatin jiha ta daina burga da zanen aro,” inji shi.

Sai dai a martanin da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta mayar Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Alhaji Isa Bajini Galadanci ya ce ya kamata in za su yi suka su yi mai ma’ana ba su buge da hassada su rufe idonsu daga abin da aka yi ba. Ya ce gwamnatin ta samar da ci gaba a Jihar Sakkwato hasali ma su zo a hada kai don ciyar da jihar gaba, kuma su sani kasafi hasashe ne.

Kan gaza biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 30, ya ce  ana tantance ma’aikatan jihar ne da zarar an kare za a fara biya “A Ma’aikatar Lafiya kawai mun gano ana biyan likita 580 albashi amma 260  ne kawai muke da su, ina sauran? Haka a wasu ma’aikatu za ka samu ma’aikaci daya yana amsar albashi wuri uku da zarar mun gyara harkar albashin za mu fara biyan mafi karancin albashin na dubu 30” a cewarsa.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya