✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta yi taro kan matsalar cin hanci a Kaduna

Jam’iyyar APC ta gudanar da taro a kan matsalar cin hanci da rashawa da yadda suke mayar da hannun agogo baya ga ci gaban kasa.…

Jam’iyyar APC ta gudanar da taro a kan matsalar cin hanci da rashawa da yadda suke mayar da hannun agogo baya ga ci gaban kasa. Taron wanda aka gudanar a dakin taro na Umaru Musa ’Yar’aduwa da ke Dandalin Murtala a Kaduna ya samu halarta shugabannin da ’ya’yan jam’iyyar na ciki da wajen jihar. A jawabin shugaban rikon Jam’iyyar APC na karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Alhaji Ahmadu Yaro Coca Cola ya ce “idan mahukunta za su magance cin hanci da rashawa su samar da ayyukan yi ga dimbin matasa, Najeriya ba ta da wata sauran matsala.” Alhaji Musa Kuriga kuwa kira ya yi ga matasa su daina siyasar kudi, saboda a cewarsa “hakan na daya daga cikin dalilan da suka jefa mu a halin da muka samu kanmu a yanzu.”  Da dama daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu a wurin taron sun tabo batutuwan da suka shafi magudin zabe da amfani da matasa don bangar siyasa da yadda jam’iyyar ke ci gaba da daura damarar lashe zabubbukan da ke tafe.