✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta yi watsi da kin yin zabe a wasu jihohi •Yunkurin amsar kujerun G5: PDP na barazana ga dorewar dimokoradiyya – APC

Jam’iyyar APC ta yi Allah wadai da kalaman da shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC) Farfesa Attahiru Jega ya yi na cewa zai yi wuya…

Jam’iyyar APC ta yi Allah wadai da kalaman da shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC) Farfesa Attahiru Jega ya yi na cewa zai yi wuya a gudanar da zaben 2015 a jihohin da ke fama da dokar ta-baci. APC ta ce wajibin gwamnati ne ta samar da zaman lafiya a jihohin ta hanyar amfani da karin wasu matakai, amma ba na soji kawai ba da ke wakana a halin yanzu
Jam’iyyar APC da gwamnatocin jihohin da ke karkashin dokar ta-baci sun soki furucin na Farfesa Attahiru Jega ya yi, inda APC ta ce da ma can tana da shakku dangane da gaskiyar Gwamnatin Tarayya wajen yaki da maharan da ke tada zaune-tsaye a jihohin.
Gwamnatocin jihohin Borno da Yobe da Adamawa sun ce rashin gudanar da zabe a jihohin tamkar sallama yankin ne ga kungiyar Boko Haram, yayin da suka zargi Gwamnatin Tarayya da kokarin hana musu shiga zabe saboda jihohinsu na karkashin mulkin jam’iyyar adawa.
Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya ce da sake game da furucin na Farfesa Jega, kamar yadda kakakinsa Alhaji Abdullahi Bego ya shaida wa manema labarai a Damaturu. Ya ce, kasancewar dokar ta-bacin wa’adinta zai cika ne a watan Afrilun badi, ya yi wuri Jega ya ce da wuya hukumarsa ta gudanar da zabe a jihohin, inda ya yi tambayar ko shugaban yana da masaniya ne cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da fadada dokar a jihohin saboda wasu manufofi?
Jam’iyyar APC ta kira taron gaggawa a Abuja a ranar Talata inda ta ce shigar da kara da PDP ta yi a kotu tana neman a kwace kujerun gwamnoni biyar da suka sauya sheka zuwa APC da cewa barazana ce ga dorewar dimokoradiyyar kasar nan.  APC ta ce PDP ta fi kowace jam’iyya cin moriyar komawar shugabannin da a aka zaba a karkashin wata jam’iyya zuwa cikinta duk da cewa wadanda ke cikinta a yanzu ba su yi gwagwarmayar kafa ta ba.
Shugaban riko na jam’yyar ta kasa Cif Bisi Akande, ya ce sauya sheka ga Gwamna ko Shugaban kasa da mataimakansu, al’amari ne da Kotun koli ta riga ta warware a baya a lokacin da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya fice daga PDP zuwa AC, kuma kotun ta tabbatar masa da kujerarsa.