✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC za ta iya rushewa bayan tafiyar Buhari – Gwamna Fayemi

Gwamnan jihar Ekiti a Najeriya ya ce jam’iyyar APC mai mulkin kasar na iya wargajewa a karshen mulkin Shugaba Muhammadu Buhari idan har ba a…

Gwamnan jihar Ekiti a Najeriya ya ce jam’iyyar APC mai mulkin kasar na iya wargajewa a karshen mulkin Shugaba Muhammadu Buhari idan har ba a dauki matakan da suka dace ba.

Kayode Fayemi, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin kasar, ya shaida wa Daily Trust cewa yana fargabar jam’iyyar “ba za ta yi tsawon kwana ba” muddum ba a samar da turakun da za su kareta ba.

Ya kara da cewa “Shugaba Buhari shi ne turken da ya daure jam’iyyar wuri guda a yanzu” kuma idan ba a “samar da tsare-tsaren da za su zaunar da ita da gindinta ba, sannan a ja kowa a jiki”, to za ta iya ka sa kai bantanta nan da ‘yan shekaru masu zuwa.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da kawunan jigagan jam’iyyar ke kara rabuwa kan makomar shugabanta Adams Oshimhole, wanda wasu ke neman a tsige shi daga mukamin nasa.

Rikin ya kara ta’azzara ne saboda yadda ta yi tsami tsakanin Oshimhole da gwamnan da ya gaje shi a jihar Edo, inda har ta kai ga wani bangare a jihar ya ce ya dakatar da shugaban daga jam’iyyar kwata-kwata.

Daily Trust ta fahimci cewa bambarwar da ake yi kan shugabancin jam’iyyar na da alaka da yunkurin neman shugabancin kasar a shekarar 2023.

Sai dai Gwamna Fayemi ya musanta hakan, yana mai cewa “babu wanda ya son tsawon lokacin da zai yi a duniya ballantana a fara maganar zaben 2023”.

A matsayina na wanda ya jagoranci kwamitin kafa manufofin jam’iyyar APC tun farko, na son cewa babban abin da zai tabbatar da dorewarta shi ne kafawa da amfani da manufofinmu”.

Ya bayar da misali da jam’iyyun da suka shafe shekara da shekaru kamar na ANC a Afirka ta Kudu, da makamantansu a Ghana da Kenya.

Alaka da Tinubu

Sai dai gwamnan ya ki amincewa ya bayyana matsayarsa kan ko ya gamsu cewa Mista Oshimhole ne mutumin da ya dace ya ci gaba da shugabancin jam’iyyar tare da samar da sauye-sauyen da yake kira a yi.

“Adams abokina ne kuma kwararre ne, mun yi gwamna a lokaci guda, amma ra’ayina ni kadai ne ba shi ne mafi muhimmanci ba, ra’ayin jama’a gaba daya shi za a duba”.

Kayode Fayemi ya kuma nace cewa babu wani sabani tsakaninsa da jagoran jam’iyyar Bola Ahmed Tinubu duk da cewa wasu na ganin basa jituwa.

Ya ce “Sanata Tinubu jagora ne, kuma dan kishin kasa, na ya aiki tare da shi tun kafin a dawo wannan zangon na demokuradiyya”, kuma ina fatan zai goyi bayan duk abin da zai kawo sauyi da inganta jam’iyyar nan.

Masu lura da al’amura na ganin rikicin na jam’iyyar APC na ci gaba da ruruwa ne duk da yunkurin shawo kansa da jam’iyyar ke cewa tana yi.