Search
Subscribe
APC za ta kada PDP a Jihar Kebbi a zaben 2015 – Argungu

APC za ta kada PDP a Jihar Kebbi a zaben 2015 – Argungu

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Sulaiman Muhammad Argungu ya ce abu ne mafi sauki a zaben shekarar 2015 su kai keyar Jam’iyyar PDP kasa a jihar da kasa badi daya.
Tsohon Mataimakin Gwamnan wanda ya rike mukamin Sakataren Tsare-Tsare na kasa na rushishiyar Jam’iyyar ANPP, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Argungu.
Ya ce, a zaben shekarar 2011  kuri’ar ANPP da CPC da ACN idan ka hada su, sun ci zabe da babbar rata kuma ga shi yanzu sun hade  wuri daya. Don haka an gama da PDP a Kebbi da kasa baki daya idan Allah Ya yarda.
Shi ma a lokacin da yake zantawa da Aminiya, wani jigo a tsohuwar Jam’iyyar CPC a Jihar Kebbi Alhaji Bashar Isa Matawalle, ya ce matasa su ne da ragamar canja gwamnati da kuri’a, saboda ana bukatar bunkasa tattalin arzikin kasa da tsaro don samun zaman lafiya da komai ba zai yiwu ba sai da shi a kasar nan.
Alhaji Bashar Matawalle ya ce, za su tashi tsaye wajen ganin an zabi shugabanni nagari tun daga kan wakilan jam’iyya zuwa kan Shugaban kasa, domin rashin shugabanci nagari ke cutar da su matasa fiye da kowa, musamman rashin aikin yi da sauran matsaloli da suke fuskanta a wannan lokaci.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin