Daily Trust Aminiya - Arewa na bin Gwamna Yuguda Bashi -Solomon Dalung
Subscribe

Arewa na bin Gwamna Yuguda Bashi -Solomon Dalung

Fitatcen malamin jami’ar nan da ke jami’ar Jos, kuma mai sharhi kan al’amarun yau da kullum , Barista Solomon Dalung ya bayyana cewa kalaman da Gwamnan Jihar Bauchi. Malam Isah Yuguda ya yi na cewa ya fice daga kungiyar Gwamnonin Arewa saboda sun ki zaben Gwamna Jonah Jang a matsayin shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya  a kafofin watsa labaran kasar nan, ba shi da wata hujja. Barista Solomon Dalung, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos.
Ya ci gaba da cewa Gwamna  Yuguda ba shi da wata hujja  da zai tsani Gwamnonin Arewa kan  abin da zai kawo ci gaban Arewa, don an ki zaben Gwamna Jang.
Ya ce Arewa ta yi wa Yuguda komai, domin an nuna masa kiyayya da rashin gata a PDP, aka  yi masa korar kare a zaben shekara ta 2007. Amma jama’ar  Jihar Bauchi suka nuna masa kauna da karamci, suka zabe shi gwamnan jihar  a jam’iyyar adawa ta ANPP. Don haka ya ce babban mutum da Arewa take bi bashi, shi ne Isah Yuguda.
Ya ce kuma  jama’a suna ganin mutuncin  Isa Yuguda a Arewa, saboda irin  karamcin da Jihar Bauchi ta yi wa al’ummomin jihohin Barno da Yobe da Adamawa da  Filato da Kaduna da suke gudun hijira a jihar, sakamakon rikice-rikicen da aka samu a wadannan jihohi. Don haka ya ce Yuguda yana da mutumci a idanun al’ummar Arewa. Saboda haka bai kamata Yuguda ya je ya shiga irin wannan al’amari  wanda zai zubar masa da mutumci ba.
“Kamata ya yi a sani cewa a Najeriyar nan, babu wanda ya isa ya hana shi abin da Allah ya bashi. Don haka ya ce  bai ji dadin kalaman da Isah Yuguda ya yi ba, kan maganar zaben shugaban kungiyar gwamnoni ta Najeriya,” inji shi.
Barista Dalung ya yi bayanin cewa Gwamnonin Arewa ba su da ikon tilasta wa wani ya jefa kuri’a. Kuma  gwamnonin suna da ’yanci su zabi wanda suke so ya zama shugabansu. Don haka, sun yi amfani da ikon da suke da shi na tsarin mulkin wajen zaben wanda suke son ya zama shugabansu.
Ya ce ya kamata Yuguda ya sani, Jang da yake fada a kansa ba mai son Arewa ba ne. Don haka bai kamata ya fito ya ce yana goyan bayansa ba.
Ya ce  Jang  ne fa  yake ta fadin cewa babu ruwansa da Arewa. Sai kuma a yanzu da za a yi amfani da shi a bata Arewa, nan ne zai ce shi dan Arewa ne?
Ya ce duk inda Jang ya tafi sai an yi fada, domin ya zama Gwamna Jihar Filato, fada ya zama kamar ruwan dare a jihar. Ya ce tun da ake zaben kujerar shugaban gwamnoni ba a taba yin fada ba, yanzu ga shi da Jang ya shiga takarar zaben  an tashi da fada.
Ya ce ko zaben shugabancin kujerar Majalisar dinkin Duniya Jang ya tafi, sai an tashi da fada a wajen, ta yadda duniya za ta shiga yaki gabaki daya, domin Jang yana yawo da fada ne a gindinsa.
To, amma a nasa ra’ayin, wani shugaban matasa a jam’iyyar PDP a karamar Hukuma Lere da ke jihar Kaduna, Malam Mahe Kwaftara ya yaba wa Gwamna Isah Yuguda kan bayanin da ya yi a kafofin watsa labarai, kan yadda suka yi da Gwamnonin Arewa akan zaben shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya. Malam Mahe Kwaftara ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake zantawa da wakilimu.
Ya ce wannan bayani da Malam Isah Yuguda ya yi, ya nuna  cewa shi dattijo ne na gaskiya kuma mutum ne mai kishin Arewa da kasa gabaki daya. Ya ce samun shugabanni irin Yuguda  zai kawo cigaba a arewa.  Don haka ya yi kira ga al’ummar Arewa su tsaya su fahimci wannan bayani da gwamna Isah Yuguda ya yi, kada su yi masa mummunar fahimta.

texem
More Stories