✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ariel Castro wanda ya boye ’yan mata shekara 10 ya kashe kansa a kurkuku

Ariel Castro, dan shekara 53, wanda aka yanke wa hukuncin shekara dubu da daya, bisa laifin boye  ’yan mata, har tsawon shekara 10,  ya hallaka…

 Ariel Castro, wanda ya boye ‘’yan mata har shekara 10Ariel Castro, dan shekara 53, wanda aka yanke wa hukuncin shekara dubu da daya, bisa laifin boye  ’yan mata, har tsawon shekara 10,  ya hallaka kansa. Mamacin wanda aka killace a wani gidan gyara halinka da ke garin Columbus a tsakiyar birnin Ohio,  a cewar mai magana da yawun wannan cibiya ta gyara halinka, JoEllen Smith ya tabbatar da an samu mutumin a rataye, inda jami’an kula da lafiyar  ’yan fursuna suka yi ta kokarin farfado da shi, amma kafin su karasa zuwa asibiti Castro ya cika.
An killace shi a wannan gida ne, domin munin laifinsa, kuma ana bibiyar halin da yake ciki a kowace rabin sa’a. ’Yan matan da ya boye, ya sace su ne a shekaru daban-daban, wato a tsakanin shekarar 2002 zuwa 2004. Kuma wadannan ’yan mata uku shekarunsu a lokacin da suka bace sun kama daga ’yar shekara 14 da 16 da 20. Sun tsira daga hannun Castro ne a ranar 6 ga Mayun bana.