✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsenal ta yi kuskure wajen sayar da Iwobi – Kanu

Tsohon Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya Super Eagles Kanu Nwankwo ya bayyana takaicin kan yadda kulob din Arsenal na Ingila ya sayar da…

Tsohon Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya Super Eagles Kanu Nwankwo ya bayyana takaicin kan yadda kulob din Arsenal na Ingila ya sayar da dan kwallon Najeriya Aled Iwobi.

Kulob din dai ya sayar da Iwobi ne ana gab da rufe kasuwar cinikin ’yan kwallo a bana a kan Fam miliyan 40 (kimanin Naira biliyan 17 da miliyan 920) ga kulob din Eberton.

Tunda Iwobi ya koma Eberton tauraruwarsa take haskakawa.

“A gaskiya kulob din Arsenal ya yi kuskure wajen sayar da Iwobi ganin matashi ne mai hazaka wanda ya iya buga kwallon kafa,” i ji Kanu.

Aled Iwobi dan shekara 23 yana daga cikin ’yan kwallon Super Eagles kuma ya shafe shekara 8 a Arsenal kafin kulob din ya sayar da shi ga Eberton.