✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asalin Hausa (3)

Farfajiyar Kasar Hausa a zamanin Kankara da Ruwan Dufana Tattaki da tuntuɓa da gawarwakin mutane da dabbobi da albarkatun ƙasa da duwatsu da ke turbuɗe…

Farfajiyar Kasar Hausa a zamanin Kankara da Ruwan Dufana

Tattaki da tuntuɓa da gawarwakin mutane da dabbobi da albarkatun ƙasa da duwatsu da ke turbuɗe a ƙasa wasu makamashin gina tubalin tarihin mazauna duniya ne. Akwai zamanin da ƙanƙara ta lulluɓe wurare da dama da tsaunuka (Glaciatios of mountains). Mahadi Adamu ya ce: “Tsaunin Ayar yana daga cikin tsaunuka da ƙanƙarewar tsaunuka ta auka wa duniyar Sahara. Ƙanƙarewa a Sahara ta ci gaba har zuwa shekarar 18 B.C. Tsaunin Ayar yana daga Arewacin farfajiyar ƙasar Hausa ta gado.”

Ashe ke nan, Hausawa (da Kasar Hausa) sun shiga yanayin ƙanƙarewar tsaunuka kimanin shekara miliyan biyu da suka shuɗe.

Wannan taƙaitaccen bayani ya kore tatsuniyar Bayajidda da aka ƙirƙira jiya. Haka kuma, zancen zuwan Gabasawa daga Makka ko Bagadaza ko Iraƙi bai taso ba, a irin shekarun da aka ambata. A wani dogon saƙon da Mahadi Adamu ya yi cewa ya yi:

“Za mu fara kirdadon haƙa tarihin ƙasar Hausa na wani lokaci (mai tsawo) kimanin shekara miliyan 430, lokacin da ƙoƙon duniyar wannan farfajiya tamu ɗaya ne, har ya soma rarrabuwa zuwa farfajiya biyar da muke ciki a yau.

Lokaci da ake zaton duniyar mutane ta mamaye da ruwa gaba ɗaya, bayan janyewar ruwan sabon kundin tarihin mutane ya fara aiki. Masu bincike sun tabbatar da cewa, garuruwan Dange Shuni da Sakkwato da Kware da Wurno da Gwaranyo da Illela da Gudu da Tangaza a mazauninsu na yanzu can da ƙarƙashin wannan makeken kogi suke. A 1920 an ƙara samun hujjojin da suka ƙarfafa wannan da’wa ta Mahadi Adamu.

Abubuwan da muka tattauna suna cewa, akwai buƙatar a sake samun wasu makaman tunkararsu. A nawa tunanin, har yanzu da sauran rina a kaba, mun dai gano cewa, ga nahiyar da mutum ya tsira. Yaya za a yi da tulin waɗannan hujjojin a sahihin tarihin Bahaushe da harshensa.

Daskarewar duniya da Ruwan Ɗufana da aka yi kowa da kowa ya shafa dole kowa ya buɗa sabon kundin tarihi. Idan za mu iya kakkaɓe wa tarihi da tahihi da tatsuniyoyin da ke yawo a bakuna da rubuce-rubuce kan asalin Bahaushe da harshensa waɗannan matakai za su taimake mu.

Matakan tantance Ƙasar Hausa da mutanenta

Mun ci nasarar gano cewa, a tarihance na masanan Yamma cewa daga biri mutum ya fara. Haka kuma, birin daga Nahiyar Afirka aka ƙago shi. Bugu da ƙari, Kasar Hausa daskarewar ƙanƙarar duniya da Ruwan Ɗufana nan ya tarar da ita. Idan haka ne, babu laifi binciken diddigin asalin Bahaushe ya fara daga wurin da aka tarar da Bahaushe ya mamaye a matsayin ƙasarsa ta haihuwa da gado da mulki. Masana wannan zamani ya kyautu su himmatu ga bibiyar diddigin waɗannan abubuwa.

Farfajiyar Ƙasar Hausa

Bincike ya himmatu ga tantance iyakar ƙasar Hausa Gabas da Yamma, Kudu da Arewa. A gano iyakakokin da ke fita wajen duniyar baƙar fata da masu ɗuruwa a duniyar Afirka. A leƙa maƙwabtan Bahaushe na arziki da na hamayya. A gano, ƙasashen da suka yi tasiri a kansu. A fayyace yaƙe-yaƙen Bahaushe da sha’anin bauta a ƙasar Hausa da kuma ƙasashen da suka yi hulɗar diflomasiyya da ƙasar Hausa. Cikin haka za a tantance sarautun Bahaushe yadda suke da yadda ake gadonsu da tuɓe su da iyakokin ikonsu. Idan haka ta samu, hoton Kasar Hausa zai fito tsaf! Za a gano baƙinta da ’yan gida da ’ya’ya da bayi da masu mulki da talakawa da kafuwar garuruwan ƙasar Hausa da sigogin sunayensu. Wannan shi ne mataki na farko da ya kamata a ce, bincike ya tunkara gadan-gadan. Waɗannan abubuwa dole sai da makaman Adabin Bakan Bahaushe za a tsattsefe su.

Duniyar Bahaushe

Tilas a himmatu ga leƙa  duniyar Bahaushe da yadda Adabinsa (Literature) da Al’adunsa (Culture) suka kamo su. Imanin Bahaushe a kan Mahaliccinsa da iskoki da ke tare da shi da Dodo da ƙirƙirarrun abubuwa da ke a farfajiyar duniyarsa, tun daga sunayensu da yadda ake saduwa da su da yadda ake hulɗa da su wasu tagogin leƙon dugin Bahaushe ne. Duk inda ɗan Adam yake, waɗannan ɗabi’u suna nan cikin jininsa. Da su ake rarrabe shi da waninsa. Adabinmu da dama sun kakkamo su a wurare daban-daban. Kafa hujja da su shi ne, warkam shiga rijiya da dawo.

Daulolin Bahaushe

Masana sun himmatu ga binciken daulolin ƙasar Hausa suka kawar da kai da zuzzurfan binciken garuruwan Hausa daɗaɗɗu da tarihin kafuwarsu. Daulolin ƙasar Hausa cibiyoyinsu na yanzu ba su ne a da ba. Daular Kanta ba a Argungu aka kafa ta ba. Daular Katsina sai an koma Durɓi-ta-Kusheyi. Daular Gobir daga wani Birnin Lalle aka zo Sabon Birni. Zamfarawa daga Rawayya aka gurgusa Gusau. Kano daga Dutsin Dala da manyan tsaunuka na sassanta. Idan aka kalli garuruwan da suka tsirar da daulolin ƙasar Hausa sosai za a gano dalilin kafuwarsu, da waɗanda suka kafa su da dalilan ƙaurace-ƙauracensu. Dukkan waɗannan abubuwa adabin mazauna garuruwan bai kawar da kai a kansu ba. Adabin kowane gari na kirari da karin magana da labarun gargajiya da waƙe-waƙen dandanli da na yara da mata da maza da manya sun kakkamo su. Dogara kacokam da tattaunawa da bayanan da ’yan leƙen asiri da ’yan mulkin mallaka da Turawan Mishan suka yi ba zai wadatar ba.

Daga Bishir Ɗanƙaura 08067384535