✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ashe a Najeriya akwai masu gaskiya da amana?

Daga fA ziyarar da na kawo Najeriya kwanakin baya daga Amurka (inda nake zaune), wani al’amari marar dadi ya faru da ni, kodayake wani direban…

Daga fA ziyarar da na kawo Najeriya kwanakin baya daga Amurka (inda nake zaune), wani al’amari marar dadi ya faru da ni, kodayake wani direban tasi ya ceto ni daga tafka mummunar asarar da ba zan taba mancewa da ita ba a duk rayuwata, da ba dominsa ba. Wannan al’amari da ya faru, tuni ya canza mani tunani game da ’yan Najeriya, musamman ma masu tuka motocin tasi.
Wani lokaci can a cikin watan yuli na bana, ni da ’ya’yana uku tare da dan abokina muka shiga wata tasi ce a Abuja. Kafin mu tashi, sai na sanya babbar jikkata a but din motar kuma Allah da ikonSa da muka sauka sai na mance da ita; dan tasi ya tafi da ita.
Jikkar nan kusan tana dauke da rayuwata, domin kuwa duk wani abu mai muhimmanci a gare ni suna cikinta. Akwai kwamfutar tafi-da-gidanka da na’urar buga takardu sabuwa da fasfo-fasfo da takardun biza nawa da na ’ya’yana da takardun shaidar na ainahi na makarantun duk da na yi, da katin inshorar rayuwa na Amurka da mabudan gidana da na mota da kuma sauran takardu masu matukar muhimmanci.
Lokacin da dan tasi ya tafi ya bar ni, nan takaici ya cika ni, na rasa ma abin da ke mani dadi a duniya. Ga shi ban san direban ba, ban san lambar motarsa ba, haka kuma ban san yadda zan hadu da shi ba. Hasali ma, ba zan iya shaida shi a fuska ba, domin koda muke tafiya tare a motar, ba mu yi wata hira da shi ba. Hana rantsuwa, lokacin da na sauka, na ba shi kudi fiye da ka’idar da ya fada mani, ya yi ta yi mani godiya. Domin idan na zo Najeriya, nakan biya dan tasi kudi da yawa, domin nakan kwatanta kudin da muke biya a Amurka, sai na lura cewa kamar ana cutar ’yan tasi ne a Najeriya.
A daren ranar nan ban runtsa ba, ina tunanin takaicin wannan asara da ta hau ni. Da safe, a tattaunawar da muka yi da Hajiya Zainab Okino, jami’a a jaridar Blueprint, wacce a gidanta na sauka, mun shawarta cewa za mu tuntubi gidajen rediyo da talabijin a Abuja, domin a cigita wannan jikka, kila a gano ta. Lokacin da za mu tafi gidan talabijin na AIT, ashe mun makara, domin shirin da ake yi na cigiya, lokacinsa ya wuce. Muna nan muna laluben matakin da za mu dauka na gaba, sai ga kiran waya daga dan uwan Hajiya Zainab, cewa ga mai tasi nan ya dawo mani da jikkata, ana jiran in je in tantance kayan ciki, ko akwai wanda babu.
Jin wannan labari ya sanya ni cikin tu’ajjibi. Nan na fara tunanin ashe a Najeriya akwai mutanen kirki masu gaskiya da amana? A ce kasar da ta yi kaurin suna ta bangaren yawaitar ’yan wankiya da marasa gaskiya amma kuma ga shi dan tasi ya maido da jikkar da ke dauke da kaya masu tsada?
A lokacin da na je na yi ido biyu da dan tasi din nan, mamaki ya kara cika ni. Sunansa Abdulrahman Dauda. Ya ce shi dan asalin garin Ilorin ne amma an haife shi kuma ya girma a Kaduna. A lokacin da na tambaye shi abin da ya karfafa masa gwiwa ya maido mani da jikkar, bai sayar da kayan ciki masu tsada ya rike kudin ba, duk da cewa shi talaka ne, sai ya ce mani: “Ta yaya zan dauki kayan da ba nawa ba kuma in maida su nawa?”
Ya kara shaida mani cewa, a lokuta da dama da suka shude, ya sha mayar wa da fasinjoji kayayayyakin da suka manta a motarsa, kamar wayar salula da sauransu. “Ni Musulmi ne kuma addinina ya koyar da ni cewa haramun ne in dauki abin da ba nawa ba.” Inji shi. “Idan har na yi haka, ba zan taba samun natsuwa a raina ba. Haka kuma a lokacin da na ga fasafo dinka kuma na gano cewa a Amurka kake zaune, nan take na ce lallai akwai bukatar in yi hanzarin maido maka da jikkar nan. Babu shakka ina tare da fain ciki, ganin cewa wannan abin da na yi ya faranta maka rai.”
Wannan halin gaskiya da amana da Abdulrahman ya nuna ya dawo mani da yakinin cewa lallai akwai ’yan Najeriya masu gaskiya, wadanda talakawa ne, da masu mulki ke masu zalunci. Wani abin mamaki ma shi ne, kafin ya dawo mani da jikkar, duk dan tasin da na gani, na yi masa batun, sai ya karfafa mani gwiwa cewa tabas za a dawo mani da kayana. Shi ne ma wani ya kara mani kaimi, ya ce ai idan da ba su gano mai kayan ba, sukan kai ofishinsu na yuniyon ko kuma gidajen rediyo da talabijin.
Bayan kwana biyu da faruwar wannan al’amari, sai kuma ga shi na gamu da labarin wani dan tasi din a Legas, wanda ya mayar da Naira miliyan 18 da wani fasinja ya manta a motarsa. A lokacin kuma Naira 800 kacal ya mallaka a rayuwarsa. Babu shakka labarin nan ya taba mani zuciya. Kuma haka ya tabbatar da cewa lallai akwai mutanen kirki masu gaskiya a sako-sakon Najeriya.