Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Ashe Turawa mutane ne? (10)

Ashe Turawa mutane ne? (10)

Duk da na samu wannan agaji ban yarda na leka waje ba, saboda tsoron sanyi.  A wannan makon idan ban da taron tarbarmu da na leka ban je ko’ina ba, sai da na kusa kwana bakwai a gida, ina shirya yadda al’amuran zama a Landan za su kasance. A kuma wannnan zaman ne na fahimci yadda rayuwar Landan da kuma Ingila take baki daya. Nakan fita in zaga don mike kafafu, wata sa’a kuma in sawo jarida ko kuma na kalli talabijin ko satilayit, amma shi ma in ka gan ni cikin kayan sanyi za ka dauka dodo ne, domin ba alamar jiki ko fuska tattare da ni.

Rayuwa irin ta Ingila ba abin da ba za ka gani ba. Abubuwan kallo dai ba sai na yi bayaninsu ba, domin kuwa ka ga na ban dariya, ka ga na ban haushi, ka ga na ban takaici, ka kuma ga na ban tausayi. A kullum sai ka dauka cewa ba abin da Turawan Ingila suka mayar da duniya in ba ta nishadi ba. Ba a dai barci na a zo a gani, domin kuwa tasoshin talabijin bude suke kullum rana ta Allah. Haka jaridunsu, tunda yamma za ka fara cin karo da wasu, wasu ma kyauta ake rarrabawa da zarar an tashi daga aiki, bakin mararraba. Da na fahimci haka, yamma na yi zan fita yawon motsa kafafu, in karbo jaridu biyu London Paper da kuma London Lite, in dawo gida in shiga karatu.

Sai dai ba abin da ke burge ni irin yadda ake gudanar da siyasar kasar, musamman tsakanin manyan jam’iyyun siyasar kasar biyu, Labour da Conserbatibe. Tun ina Najeriya ni dai magoyin bayan Jam’iyyar Labour ne, saboda tun da shugabanta, Tony Blair, ya ci zabe nake biye da ita. Kada ka fara tambayata me ya hada ni da Jam’iyyar Labour kuma, ni da ke Najeriya. Domin in ka yi mini irin wadannan tambayoyi, sai in ce da kai me ya hada dan Najeriya da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ko kuma Arsenal ko Chelsea? Har ma ka sa na tuna da wannan batu, amma zan dawo kan wasan kwallo nan gaba, ma tattauna shi ma.

Duk da ba a yi tambayar ba, bari in amsa, ba wani abu ya hada ni da Jam’iyyar Labour ba  sai manufofinta da ke da’awar agaza wa  ‘talaka’, ni kuma duk mai irin wannan manufa ina shiri da shi ko ita ko kuma su. Shi ya sa ma ba inda na fara ziyarta a ranar Lahadin farkon zuwana a watan Oktoba a Landan sai kabarin Karl Mard, shugaban talakawan duniya! Shi ma zan dawo kan wannan batu nan gaba. Yanzu mu koma kan batun siyasa da ’yan siyasar Ingila tukuna.

Daidai lokacin da muka iso Landan shugaban kasar Ingila shi ne Gordon Brown, shi ne ya gaji Tony Blair bayan ya sauka don kashin kansa bayan shekara 10 yana mulki. Duka-duka Gordon Brown bai wuce wata uku a karagar ba, muka iso Ingila. Abin da ya ja hankalina game da siyasar shi ne yadda ’yan adawa suka sa shi gaba a karkashin jagorancin Dabid Cameron na Conserbatibe, sai ka dauka cewa ya kashe masa uwa ne. Kullum rana ta Allah ba ka jin komai sai Gordon Brown ya kasa, ko ya gaza, ko bai iya mulki ba, ko ya yi kaza mara amfani. Ni da farko sai na dauka cewa ai talabijin na BBC da ITB da Channel 4 da ma wasu da dama ko dai na Jam’iyyar Consrbatibe ne ko kuma ’yan jaridar suna goya wa Jam’iyyar Conserbatibe baya ne a boye.

Me ya sa na ce haka? Kullum rana ta Allah ba sa komai sai darzar wannan bawan Allah. Da kuma ya yi kuskure ya ce yana son ya kira zaben gaggawa domin ya gwada farin jininsa, kai ka ce za a cinye shi danye, ya kira din mana, ai shi zai ji kunya in ji ’yan adawa. Da ya hango cewa in ya kira zaben nan ba zai kai labari ba, ya janye, kai ka ce ya zagi Sarauniya ce. Ni na tabbata bai yi barcin kirki ba a cikin kwanakin na watan Oktoba. Tun ina jin haushin ’yan adawar, saboda sun matsa masa, sai daga baya na fahimci cewa ai dimokuradiyyar ke nan!

Ba ma inda abin ya fi burge ni, sai yadda suke gudanar da wani zaman majalisa inda suke kiransa  na ‘Amsa Tambayoyin Firayi-Minista,’ na kosa ranar ta zo, domin kuwa kowa na da ikon ya je wurin kallo ko kuma ya kalla a talabijin kai-tsaye. Na ce a raina, bai yi kuskure ba, sun nemi su cinye shi danye, ina kuma ga shi ya yi baram-baramar kiran zabe, ya kuma bultse! Haka kuwa aka yi wannan rana, sai da Gordon Brown ya ba ni tausayi, in da a irin Najeriya ce na san cewa sai ya yi gumi sharkaf, amma da yake sanyi ake yi bai yi gumin ba, amma yadda hannayensa ke bari, kai ka san ya sha da kyar.

Wannan abu ya sa mini tunanin cewa anya kuwa tsarin dimokuradiyya muke bi a namu yankin na Najeriya ko Afirka ko wasu sassa na kasashen da ke neman ci gaba!

Kamar yadda na fara bayyanawa a baya, tunda dai na yi wajen mako ban leka ko’ina ba, sai kalle-kalle da yawon mike kafa, zama a cikin gida sai ya zamar mini matsala daga baya, ya kuma fara ginsa ta. Can sai na tuna cewa ai Angelica, Sakatariyar Cibiyar da muke ta ce idan ina neman abokin hira ko yawo to in buga mata waya, na ko kira ta, na ce tana da lokaci da za mu leka cikin gari, in ba ido abinci? Nan take muka ajiye za ta zo ta dauke ni cikin motarta, ranar Lahadi da safe.

Za mu ci gaba