Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Ashe Turawa mutane ne? (12)

Ashe Turawa mutane ne? (12)

Da jin haka nan take na ce mata ni dai wurare ukun da ke raina da nake son ziyarta su ne Jami’ar Odford da Cambridge, sai ko makwantar Shakespeare da ke Stratford-upon-bon, nan take ta rubuta a littafinta na daukar batutuwa don gobe.

Saboda haka daga karshen watan Satumba zuwa farkon watan Oktoba ba abin da na sa gaba sai karatu da bincike a dakin karatu na SOAS da kuma shiga Intanet domin neman bayanai. Wallahi na dauka cewa hutu na zo yi a Ingila, amma cikin wannan lokaci na fahimci cewa ba hutu na zo ba, aikin ma da nake yi har ya fi na gida Najeriya. To amma da yake ina mai kishirwar kayan aiki, ban yi wata-wata ba, na shiga gonar da take cike da yabanya mai amfani.

Ana saukowa daga masallacin Idin Karamar Sallah, na yi ban kwana da zaman gida, na tare a jami’a, ina aikin da na jefa kaina a ciki. Ina jin dai duk wani aikin bincike da ba mu da shi a gida game da Arewacin Najeriya ko dai na zuba shi a Flash Dribe ko kuma na kwafe shi a takarda ko na sauke shi cikin kwamfutata kai-tsaye. Sa’annan ba harkar adabi na mayar da hankali kadai a kai ba, duk wani abu da ya shafi Arewa, ko dai adabin ko tarihi ko harkar harshen Hausa ko Larabci ko Ajami ko addinin Musulunci ko siyasa ko kimiyyar Jogurafiyya ko sanin halin dan Adam; kai in dai takaice maka labari, ba fannin da ban taba ba. Shi ya sa ni ma na ce ai na hada dan karamin dakin karatu na kaina da kuma dalibai da hannayensu ba za su kai gare su ba.

A daidai wannan lokaci da muke ta fama da karatu da bincike, muna kuma shirya kasidun da za mu gabatar da kuma shirin zuwa ziyarar bincike. Na dai soma da Jami’ar Odford ne. Mun yi cewa zan kwana uku ne domin kalato abubuwa a  dakin karatu na Bodleian na Jami’ar da ke dauke da abubuwan da suka shafi Afirka da Kwamanwels, da hannu ko ido bai taba kaiwa gare su ba balle ya gani. Amma saboda yawan abubuwan da na ci karo da su, dole sai da na kwana shida. A can ne kuma na hade da Jane da Michael, ’ya’yan Dokta R. M. East, wanda muke yi wa lakabi da ‘Kakan Kagaggen Labarin Hausa’, sun ko zo halartar kasidar da Farfesa Furniss ya gabatar ne kan mahaifinsu, East, ni kuma da yake jika ne gare shi, ganin shi ya koyar da Abubakar Imam, wanda shi kuma ya kasance uba (na fagen adabi) a gare ni, sai na zama abin kallo. An tattauna batutuwa game da East da kuma rayayyen kagaggen labarin Hausa da ya gadar mana, kowa kuma ya yaba da gudunmawar da muka zo da ita.

Bayan mun dawo gida Landan, mun shiga halartar tarurruka na Cibiya da Sashen Tarihi da na Harkokin Cimaka da Kudancin Afirka da na Cibiyar Kungiyar Rainon Ingila da Kamfanonin Wallafa Littattafai, duk a Jami’ar Landan, a SOAS da kuma na sashen nazarin dabi’un dan Adam na Unibersity College, Landan da ake yi kowace ranar Juma’a. Haka kuma mun leka tarurrukan Jami’ar London School of Hygiene da London School of Economics, daga baya kuma na karasa zuwa Jami’ar Cambridge, inda can ma na kwana biyu a cikin makeken dakin karatun jami’ar na kuma gabatar da kasida kan Ruhin Adabin Kasuwar Kano wato  Publics and Spaces and the Kano Market Literature.

A cikin watan Nuwamba ne muka soma aikin da ya zame mana dole, wato biyan bashin cibiyar da ta kawo mu Landan, wato gabatar da wani abu daga cikin aikin binciken da muka yi na wata uku. Ni dai a ranar 30 ga watan Nuwamba 2007, na gabatar da kasida ta farko mai taken Behind The Beil Of The Silent Sisters: The Images Of Space, a Paradod Of Plenty And Women’s Writing From Northern Nigeria’, wani bangare ne na littafin da na kammala a lokacin wannan zama na Ingila, wanda ya tattauna matsayin mata marubuta a Arewacin Najeriya.

A ranar 6 ga watan Disamba kuma na gabatar da kasida ta karshe daga cikin littafina na biyu da na kammala mai taken The outpouring of literary Masterpieces:The Publics and the Pribates in Hausa Poetry.

Kammala wadannan kasidu ya tabbatar mana cewa mun kawo karshen wannan zaman bincike, sai kuma muka sa kai wajen yawon bude-ido, duk inda ba mu je ba a baya, muka leka. Mu ne kallon Big Ben, agogon nan da ke buga lokaci a ji shi daga nesa a duk fadin Landan. Dakunan sayar da littattafai, musamman Waterstones, inda na zama babban kwastoma, domin kuwa tuni na aiko da kwalaye shida na sababbin littattafai da na yiwo guzuri, ko dai sun fito a 2007 ko kuma za su fito a 2008, amma tuni suna kasuwa a Ingila. Mu ne a National Archibes, Gidan Sarauniya da kasuwannin Dalston da na Liberpool Street da Odford Street da uwa uba shagunan Harrods da Mark and Spencer da Clarks, kai abin ba ya lissafuwa. Da yake kuma na zo da kumar sai na leka inda kungiyar kwallon Arsenal ke wasanninta, sai da na shiga unguwar, na ga filin Emirates, amma ban samu damar ganin wasa ba, domin kuwa duk makon da za su yi wasan ko dai ba na gari ko kuma an saye tikitin da dadewa, ni kuma ba na iya sayen na bayan fage, domin ya yi tsada. Duk da haka na sawo wa dana kwallon Arsenal da duk wani abu na tarihi na kulob din, duk da cewa shi dan kungiyar Chelsea ne a yanzu. Mun dai yi cefane gwargwado, mun kuma kashe kwarkwatar ido, saura sai mu bayar da labari nan gaba!

Saura da me mun zo Ingila, zama ya yi dadi, an karu da Turawa, sun kuma karu da mu. Mun gani, mun karanta. Mun gani, mun tattara. Mun gani, mun kuma adana, domin amfanin kanmu da na baya masu tasowa. Saboda haka, ranar Juma’a 14 ga watan Disamba muka kamo hanyar gida Najeriya. Da misalin karfe 10 da rabi na dare muka bar filin jirgi na Heathrow da ke Landan, muka sauka  filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 5 da minti 25 na asubar ranar Asabar, cikin yardar Allah, domin saduwa da iyayenmu da iyalanmu da ’yan uwa da abokan arziki da muka rabu da su har tsawon wata uku. Alhamdu lillah.

 

Mun kammala