✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ashe Turawa mutane ne?  (2)

Sai da na zauna bisa kujerata ne na fahimci cewa na yi aiki da tunanina na dan Najeriya ne, ba wanda ke niyyar zuwa Ingila…

Sai da na zauna bisa kujerata ne na fahimci cewa na yi aiki da tunanina na dan Najeriya ne, ba wanda ke niyyar zuwa Ingila ba, da kuwa an tafi an bar ni, domin kuwa na hangi wata Baturiya dauke da jakar wani, tana cewa wannan mun yi ‘uploading’ dinsa. Na yi ajiyar zuciya na ce, ni ma da haka za a sauko da kayana, idan da na kara minti daya. Domin kuwa cikin ’yan mintoci, jirgi ya shirya, ya natsa, ya janye bakinsa daga jikin kofa, ya yi ribas, ya nemi hanyar fita; ina duba agogona kuwa na ga takwas da minti ashirin da biyar, ko kafin in ankara muna bisa iska, dokin Bature ya yi sama da mu zuwa Ingila, cikin lokacin da aka ce, bisa lokacin da aka tsara, kuma ba tare da jiran wani ko wata ko wadansu ba!

Wannan shi ne abu na farko da na fara yin la’akari da shi game da zuwana Ingila da kuma nazarin rayuwar mutanen da na iske a can. Wato dole ne in canja daga bakar fata zuwa Bature, ko ina so, ko ba na so! Amma shin zan iya?

Idan na ce zan kasance bakar fata kamar yadda aka san ni, to akwai matsala, domin kuwa ban san inda za ni ba, ban kuma taba tunanin ga yadda rayuwarsu take ba, sai wadda na karanta ko kuma na gani a cikin jarida ko talabijin. To amma da yake Allah Ya nufa na kasance da hakorana 32 ba 12 ko 24 ba, na san cewa ba yadda za a yi in gaza, sai dai in abin ya fi karfina. Sai dai tun a cikin jirgi na fahimci cewa ai ni ma za a iya yi da ni, domin kuwa da shigata wani katon Bature ne ya tarbe ni, ga ni cikin babbar riga shake da kwamfuta a kafada, sai zazzare idanu nake yi, ya nemi in ba shi tikitina, na mika masa, ya duba, ya ce in bi hannun dama, in wuce daki na daya, zuwa na biyu, a daki na biyu in kirga kujera ta uku, in duba dama zan ga kujerata. Ka san dan gogan, kullum a cikin adabi yake, nan yake kwana da tashi, nan take sai Abubakar Imam ya fado mini a rai, na tuna lokacin da ya je neman Ruwan Bagaja a rijiyar Sinaini da aka ce da shi, ‘da shigarka za ka ga dakuna goma sha biyu jere. Ka kidaya daki na biyar daga hannun dama ka shiga na shida’, shi kuwa ya kidime ya kidaya na hudu daga hannun hagu, ya shiga na biyar, ya sha kashin da bai taba zato ba.

Nan take sai na ce bari in yi wa kaina kiyamullaili, in shiga dakin farko, na ga kusan ba kowa, sai mutane kalilan, ban ma tsaya ba, sai na nufi na biyu, nan ne  na fahimci lallai kila na iya zama a nan, domin jama’ar da dan dama, duk da haka ina taka-tsantsan kada in karya doka, ni ma a yi min ta Imam. Na kirga zuwa kujera ta uku, na duba hannun dama, sai na ga lambar tikiti na 16, a,b,c, sai dai a bisa lambar kujerar 16c wadda ke rubuce a kan tikitina, wani bakin fata ne dan uwana zaune a kanta. Sai dai da ganin na yiwo kansa, sai ya shiga ba ni hakuri, yana tambaya ko wannan ce kujerata, na ce masa ehh kurum, ya fito daga ciki, domin tana kusa da taga ce, ya zauna a kujera mai dauke da lamabar 16a, tsakiyarmu kuwa kujera ce mai lamba 16b, ba kowa zaune a ciki.

Bayan na natsa ne sai na gane cewa ai bai san kowace kujera da mai ita ba, ya nuna mini tikitinsa yana murmushi, na ga ashe Ibo ne, shi ma za shi Ingila wajen ’yarsa hutu, kamar yadda ya gaya mini. Da muka fara tadi ne na fahimci cewa ashe ni ma na fi wadansu wayewa, ban san abin da zai sa gabana ya rika faduwa ba, ga wani da ya fi ni kauyanci. Ya fi ni mana, domin kuwa sa bel ma ni na koya masa. Jawo da turke kujerar cin abinci, ni na nuna masa. Cike takardar magireshin ni na kwatanta masa. Kai ko abinci da ake badawa a jirgi, duk da cewa azumi nake yi, sai ya ga abin da na amsa shi ma yake amsa, nan take sai na ji wani sabon karfi ya shige ni, na yi addu’a, na shiga nazarin yanayin jirgin, ashe in akwai mai daburcewa to da alama ba ni ba ne!

Ko kafin na soma nazarina sai ga wani Bature ya zo tsakiyar dakin da muke zaune, ya ce da mu jirgi ya cika, na duba na ga cewa ko a dakin da muke akwai sama da kujera ashirin da ba a zauna ba, ta yaya za a ce ya cika! Ban dai ce komai ba, domin tunanina ai su ke da asara, ba ni ba, idan suka tashi ba a cika ba, ni dai a kai ni Ingila kurum! Ashe ni ne dai ban san inda nake ba, su a tsarinsu idan kowa ya shiga jirgi, to ya cika ke nan, ba wai irin namu ba ne a Najeriya da kila in ba a samu fasinjoji da yawa ba a dage tafiyar ko kuma in ka shiga bas ko moluwe a rika yawo da kai ana neman fasinja, sai an cika ko kuma sai an bata maka lokaci kafin a tashi. Su a nasu tsarin, da zarar kowa ya shiga, to ba jira sai tafiya ko da kuwa da rabin jirgin ne ba a cika ba.

Da Baturen nan ya gama zagaye ne sai ya ce da mu, duk mai son ya sake wurin zama yana iyawa, a halin yanzu. Wadansu suka tashi suka caccanja, ni dai ina zaune, bare kuma makwabcina da ya dogara gare ni.

Wani abu da na soma tunani kansa game da Turawa shi ne ba su damu da hakkin makwabtaka ba, kila kuma ba su damuwa da halin da wani yake ciki ba. Kujerar da ke gabana dai Bature ne zaune a ciki, haka ta bayana, in na duba baya ina yi wa wannan Baturen murmushi, sai dai in ga ya yi mini yake, in na nemi mu yi tadi, sai na ga ya shiga bidar jarida, wai karatu zai yi. Shi kuwa na gabana, kwanto kujerar ya yi ta hau kafafuna, da na daga na yi masa magana, sai na ji ya ce ‘sorry’ amma bai canja zaman kujerar ba, da na ga ya mai da ni wawa sai na yi masa gula da gwiwata, ta yadda ba zai iya kwantawa da kyau ba, dole ta sa ya mayar da kujerar yadda take, ni dai ban ce komai ba. Sai da na je bayan gida, na dawo zan zauna, sai na ga yana kallona, yana yake da yake ni ma na koya sai na yi masa yaken,  kamar yadda na ga suna yi. Na shiga kujerata na kishingida na kama shirin barci.

Ban so in yi barci ba, amma da yake na kwana a Najeriya ban yi barcin ba, ka san halin barawo ban san lokacin da ya sace ni ba. Na dai farka ne a lokacin da ake rarraba abincin rana can wajen karfe daya na rana.