✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ashe Turawa mutane ne? (3)

Ba ma wani abu ne ya farkar da ni ba sai yawan motsi da kuma kalaman ‘yes what do you want’ da kuma ‘thank you’…

Ba ma wani abu ne ya farkar da ni ba sai yawan motsi da kuma kalaman ‘yes what do you want’ da kuma ‘thank you’ da ‘you are welcome’. Ganin yadda Turawan ke fadar wadannan kalamai suna bi layi-layi, kwararo-kwararo ya ba ni dariya, domin kuwa na tabbata ba su san abin da suke fada, idan kuma sun sani, kila sun haddace ne kurum, domin kuwa da alama abin da suke fada ba shi ne a zukatansu ba. Me ya sa na fadi haka?  Idan kana kallonsu za ka ga cewa suna cewa ‘me kake so’ cikin murmushi, amma ba annunri a fuskokinsu. Suna cewa ‘na gode’, amma ba alamun godiya a fuskokinsu. Suna cewa da kai “sannu kadai ko maraba,’ amma ba tabarma a hannunsu. Sai daga baya da suka dawo rarraba lemo da ‘ti’ na kara fahimtar cewa ai wadannan Turawan haka suke kamar butunbutumi, duk abin da suke fada, suna fada ne kurum, ban tabbata ko sun amince da shi ba. Sai da na isa Ingila ne na ga ko’ina kalaman ke nan, na kara fahimtar cewa, ashe al’ada ce kurum, ana fada ne ba wai don an amince da tunanin ba, kamar dai mu ne da ‘ina kwana’, ‘ina wuni’ ko da kuwa muna gaisawa da makiyanmu ne ko abokan adawa.
Kusan dai awa biyar muka yi a sama, ko dai mu yi sama sosai ko mu dawo kasa kadan, wata sa’a muna iya hangen kasa ko dai malelan ruwa ko alamun dazuzzuka, sai dai abin jin dadi shi ne kana iya bin yanayin tafiyar jirgin tun daga barin mu Abuja har zuwa Landan. A gaban kujerata akwai talabijin mai nuna sinima iri-iri, yana kuma nuna mana taswirar inda muke da sauran awoyi da kilomitoci ko mil-mil da ya rage mu isa Landan. Kana ganin yadda muke wuce sararin samaniyar kasashen da ke kan hanya. Ga mu nan mun wuce Habasha, mun shiga Maroko, mun ratsa kogin da ya raba Afirka da Turai, ga mu nan mun taso wa Turai, mun wuce Andalus, mun kama hanyar Ingila, mun shigo Ingila. Haka dai a cikin talabijin duk tsawon tafiyar nan. Da kuma muka iso cikin sararin duniyar Ingila nan ma aka fara bayyana mana. Ga mu nan mun kama hanyar birnin Landan, mun shigo sararin birnin; ni dai ina biye da taswirar nan kamar addini, sai da na ji matukin jirgin na cewa ‘wadanda ke hagu da ni idan sun leka za su hangi kogin Thames na birnin Landan a kasa,’ sa’annan na dawo cikin jirgin da yake a hagun nake kuma bakin taga, na hanga sosai na ga Landan daga kasa, abin da ya zo mani a zuciya shi ne su har yanzu a Ingila kiliya hannun hagu ne, domin motocin da ke tafiya a kasa duk ta hagu na hango suke kiliya. Wani abu kuwa da ya sake zo mani a zuciyar shi ne ga ni ga Turawan Mulkin Mallakar Najeriya, ko yaya za ta kaya? Sai mun sauka, ma ji yadda ta kaya!
Sauka daga sama ba ta zama mana matsala ba, ta yaya za mu yi maganar matsala alhali tun da muka taso daga Abuja ba wata tangarda ko matsala da muka fuskanta. Ni dai har muka iso birnin Landan ban ji inda jirgin ya yi wani motsi na tayar da hankali ba, na dauka ma cikin gidana nake, domin kuwa ba na komai daga kallon talabijin sai kallon taswirar nan ta inji da ke gabana, sai kuwa wake-wake da ke fita daga rediyo da ke boye, ka sa lasifika a kunne ka yi ta kwasar sauti iri-iri.
Bayan gida kuwa ai ba bayan gidan kurum yake ba, ga shi nan a tsakiyar daki kowa ke so sai ya leka. Yawo kuwa a cikin jirgin sai inda ka tsaya ko inda aka ce ba a shiga, amma mike kafafu bai zama matsala ba. Inda matsalar ta somo shi ne wajen saukowa daga jirgin, domin da muka iso filin jirgin Heathrow da ke birnin Landan da misalin karfe 3 saura minti biyar kamar yadda yake rubuce a cikin tikitinmu, mun dauka cewa ai sai gida kurum, to ba haka abin ya kasance ba. Mun yi  awa shida da minti 25 a sama, amma sai da muka yi kusan awa biyu a filin jirgin saman kafin mu fito daga cikin jirgin da kuma kammalawa da ’yan kwastam da magireshin.
Ba wai wata matsala ba ce irin ta lalacewar jirgi ko halin ’yan kasar ko kuma an nuna mana wani bambanci ko son kai ko makamancin haka ba, ko alama! Abu na farko dai shi ne ko da muka iso filin jirgin na Heathrow cike yake kamar kullum, da ma kafin mu iso na samu bayanin cewa akwai cinkoso a filin jirgin.
Shi dai wannan filin jirgi yana daga cikin filayen jiragen sama na duniya da suka fi kowane arangama da jirage da kuma fasinjoji, kusan duk minti guda sai jirgi ya sauko ko  ya tashi. Saboda haka koda muka iso matukin jirgin cewa ya yi da mu, sai mun dan yi hakuri domin akwai cinkoso, an ce da shi ya jira daga bakin inda ya dira na dan wani lokaci. Mu dai muna nan a cikin jirgi sama da minti 30, can sai ka ji jirgin ya motsa, ya dan yi gaba na wani lokaci, sai ya tsaya kuma na wani dogon lokaci, kamar dai wanda ya hadu da go-sulo a Legas ko bakin  titin Ahmadu Bello da ke Kaduna ko kuma bakin Bata a Kano. Da yake jirgi ne ba mota ba, sai abin ya ba ni dariya, na ga, ga mu a birnin Landan amma ba hanyar fita, bare shiga.
Da na gaji da sauraren rediyo sai na koma kallon waje in ga me ke faruwa, nan ne na fahimci cewa ai ba laifin jirgin ba ne, ba kuma na ’yan kamasho ko yuniyon ba ne (ina dariya) kamar wanda ke tashar Kuka a Kano ko Kawo a Kaduna, inda direba ko ’yan yuniyon ke yin yadda suka ga dama da fasinja. Nan dai ga mu zazzaune, jirage kuwa wannan ya tashi, wani na biye, wani na sauka, wani na biye, har ta kai ina tunanin yaya ake ba sa yin karo da juna ko kuma su fado wa juna, ganin cewa kusan a cikin kowane minti ne abubuwa ke aukuwa.