✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ashe Turawa mutane ne? (4)

To amma kamar yadda ake cewa ‘Nasara asarar duniya’, ni sai na ji zuciyata na raya mini, ‘Nasara nasarar duniya.’ Eh, to nasara man tunda…

To amma kamar yadda ake cewa ‘Nasara asarar duniya’, ni sai na ji zuciyata na raya mini, ‘Nasara nasarar duniya.’ Eh, to nasara man tunda kuwa na tabbatar idan da wadannan jirage a Najeriya ko Ghana ko Libya ko Kenya ko wata kasa da ba ta nakalci harkar yadda ya kamata ba ne, da sai dai mu rufe idanu a lokacin da jirage ke ta arangama da juna, kila wannan ya danne wancan ko kuma su yi ta karo a sama, Allah Ya tsare!.
Mun samu kusan awa daya a cikin jirgin, muna matsawa a hankali zuwa inda za mu sauka domin mu ba wadanda ke sauka ko tashi fili su ji dadin jirgawa. Can sai muka ji matukin jirginmu ya ce da mu, mun samu sarari, saboda haka ya ingiza a hankali har ya sa hancin jirgin bakin kofa, daidai matakalar da za a sauka. Ya ja ya tsaya, na gaba suka fice, mu da ke baya muna biye, kowa ya shige ciki muka fito daidai Terminal 4, kamar yadda aka tanada a tikitinmu.
Ganin yau ga ni kafata a Landan, sai na gyara babbar rigata, na bude hajar mujiya domin na ga yadda abubuwa suke, domin kuwa na tabbtar zan bayar da labarin wata rana. Sai dai kuma na ga ai ba wani abin bayar da labari a wannan lokaci, in ban da in ce tsabta dai ba sai an ce ba, filin jirgin ya birge ni kwarai matuka, nan take kuma na fahimci cewa ba zai yiwu in kasance dan Najeriya ba a irin wannan yanayi, domin kuwa ni zan ji kunya. Saboda haka nan take na shiga taitayina.
Sai dai abin mamaki tunda farko na dauka zan ga an yo mana caa kamar za a cinye mu danyu ganin ga baki sun iso, musamman yadda ake ta yayata cewa duk bakon da ya isa Landan yana shan bincike da kalailaicewa daga ’yan kwastam da migereshin, ni sai na ga abin ba haka yake ba. Da muka sauka ba wanda ya ce da mu uffan, abin da kawai ke yi mana jagora shi ne alamu.‘Ga inda za ku bi ku dauki kayanku. ‘Ga inda za ku shiga ku yi bayan gida.‘G inda za ku yi wayar tarho. ‘G inda za ku yi tambaya in kun bace.‘Ga inda za ku fita ko za ku shiga.’ Ga dai alamu nan barkatai.
Na hadu da mutum na farko ne da ya tanka mani a bakin kofar fita waje, dan migereshin ne, duk mun yi layi, da an zo kanka sai ka je gaban wanda ya kira ka ku gana. Keji-keji ne ya kai sha biyu. Ina nan tsaye har aka zo kaina, na isa wajen mutumin, wani Ba’indiye ne, nan ne kuma na fahimci cewa yawancin duk wadanda ke wurin Indiyawa ne, ba ma wannan ba sai da na yi kwanaki a Landan sa’annan na fahimci cewa ashe mutanen da nake ta hulda da su ba ma Turawan Ingila ba ne, kodai na wata kasa ko kuma bare, musamman da yake jar fata ce ko’ina. Ina kammalawa da shi na shige domin neman kayana.
Da yake ni zuwana na farko ne ba abin da na yi sai bin alamun nan, har na kai ga inda zan dauki kayana. Nan ma ban ga ’yan-ga-dako ba, sai na san cewa nan fa kowa-tasa-ta-fisshe-shi ne, saboda haka na saba jakar kwamfuta, na gyara babbar riga, na sa ido bisa gare-garen da ke wulliyo jakunkuna kowa na daukar nasa. Nan na rika jira domin kuwa sai da jakata ta wuce sau biyu ban kama ta ba, sa’annan na cafke, na yo waje da ita, na sa ido kuma na hango jakar litttattafai da takardu, ita ma na yi wuf na tsinto ta daga taro, na samu amalanke na dora su a kai, na shiga turawa, har bakin kofa, kamar dan dakon da ke cikin kasuwar Sabon Garin Kano ko ta Sakkwato ko kuma Kasuwar Barci a Kaduna.
Da yake ba wanda ya damu da wani, sai na gane cewa ai ni ne na damu kaina, domin kuwa da alama kowa da ke nan dan dako ne! Sai dai ni abin da ya zo man a zuciya shi ne  shin ba wanda ya damu da barayi, domin ba kowa a wurin daukar kayan, balle a ce za su duba abin da mutum yake dauka, su tabbatar cewa nasa ne. Kowa na tsaye ne, yana rike da lambar akwati ko jaka ko ma dai me yake tafe da shi, da ya hango nasa, ya jawo nasa, ya duba in sun dace da lambar da ke hannunsa, ya ja, ya yi gaba! Da alama dai sun amince kowa zai yi abin da ya dace! Haka kuwa aka yi, kowa ya yi abin da ya dacen, aka watse.
Sai da na zo bakin kofa ne na fara turaddadin ko zan iya kai kaina gida kuwa, wato masaukin da aka tanadar mani! Ba dai wanda ya zo tarba ta daga Jami’ar Landan, domin sakonsu da ya zo gare ni tun ina gida shi ne, ‘ka sa fam 50 a aljihu, da ka iso filin jirgin Heathrow ka shiga jirgin karkashin kasa ya kai ka tsahar Russell Skuare, daga nan ka shigo tasi zuwa jami’a, idan ka zo za mu biya ka kudin jirgin da na tasi.’ Ni dai ban amince da wannan shawara ba, ta yaya zan sa fam 50 a aljihu, idan ta fadi fa wa zai agaza man! Ta yaya kuma zan nufi jami’a idan an tashi fa wa zai tarbe ni, tunda da yamma za mu sauko? Saboda haka na yi canjin fam hamsin gida hudu, na rarraba su a aljifai hudu, na ce ko dan sane ya yanke mani aljihu dole ya bar ni da wani abu, ma’ana dole dai in samu kudin zuwa gida ko masauki. Saboda haka ko da na zo bakin kofa tunanina shi ne ban dai taba shiga jirgin kasan karkashin kasa ba ta yaya zan gane abin da ban san kansa ba! Don haka na ba kaina shawarar in bi tasi tun daga filin jirgin sama har masauki.