✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ashe Turawa mutane ne? (5)

Ina ganin layin tasi kuwa sai na ce da direba yaya za a yi, ya ce da ni ina zuwa, na mika masa adireshin masaukina…

Ina ganin layin tasi kuwa sai na ce da direba yaya za a yi, ya ce da ni ina zuwa, na mika masa adireshin masaukina da ke Goodenough College, WC1, Meckleburgh Place a tsakiyar birnin Landan, ya dube ni ya ce ‘kudinka zai iya kamawa Fam 60’, ba tambaya ya yi ko zan iya biya ba, domin su ba caji suke yi ba, ba aune ne suke yi ba, mita ce ake amfani da ita, awar da ka yi a cikin tasi, ita za ka biya, ba irin Najeriya ba da ake yin farashin daga ina, zuwa ina. Nan take na ce ya zuba kaya cikin mota, da ni da kayana muna bayan tasi, na hakince, shi kuwa ya sa hannu ya balla mitar tafiya, muka tsunduma cikin birnin Landan.

Da yake ban san ko’ina ba, sai na kasance tamkar bakauye, ni dai ina zaune, duk inda zai kai ni, ya kai ni; ko mayanka ko wani surkuki ko wajen ’yan fashi ko kuma gida kamar yadda muka yi alkawari da shi, ni dai ban da zabi.

Mun yi sama da awa daya da rabi muna tafiya, ina yi ina kallon mitar tafiyar tasi har muka iso daidai inda yake jin masaukina yake, in duba haka kuwa sai na ga Goodenough College, sai na yi ajiyar zuciya, zan sauko ya ce da ni ‘kudinka fam 55 (Naira dubu 14 da 500) kudin Najeriya.’ Na dubi mitar da ke kusa da madubin kallon baya, na ga haka ta bayyana, na sa hannu aljihu na dauko kudi na ba shi, ya ba ni canji, na sauke kaya, ya ja ya wuce ba ko sallama! Na ce lallai kudin tasi a Landan ba abin wasa ba ne. Daga filin jirgi zuwa gida kawai ya yi daidai da kudin jirgin sama daga Sakkwato zuwa Abuja!

Ni dai ba abin da ya tayar min da hankali ko nawa ya caza, don na san ban da asara domin biyana za a yi. Sai na fara jan kaya har na isa wurin tarbar baki na otel din makarantar. Ina bayyana wa ’yar budurwar da ke kan kanta ko wane ne ni, ta buga kwamfuta, ta dube ni ta ce ba nan ne masaukinka ba, sai na yi jigim na ce ashe zaune ba ta kare ba, ta ce masaukina ai yana a London House ne. Na tambaye ta ina kuma ne London House, ta ce da na fita in yi dama ga katon gini can a tsaye, to can ne.

Nan take na sake kwasar kayana na nufi can, shi ma kamar inda na fito, nan ma wata ’yar budurwar ce na iske a kan kantar, na yi mata bayani, ta buga kwamfuta, ta dube ni, ta ce tana zuwa, ta shiga wani daki ta fito, ta zo mini da wani fom na cike, na sa hannu, ta miko mini mabudi, na duba na ga hawa na daya ne, daki na 140 can ne dakin nawa.

Na ja kayana sai sama, domin da alama ban ga za ta kama mini kai kayan sama ba. Ko daga kai ba ta yi, balle ta kalle ni, na bidi matakala na hau, na nemi daki na 140, sai na ga an rubuta nan ne masaukin Oliber Twist, sai na yi dariya, na ce ashe suna bayar da daki ne bisa irin matsayin mai kwana a ciki, domin kuwa Oliber na daga cikin manyan marubutan duniya da na karanta littattafansu, saboda haka marubuci ne ya zo inda marubuci yake, Ali ya hadu da Ali ke nan!

Ina shiga cikin dakin sai na fahimci cewa ba daki ba ne kamar yadda nake tunani, dan karamin gida ne! Ga dai dakin kwana can gefe da babban gwado da ke iya daukar mutum biyu komai girmansu. Ga wani dan karamin falo can da firij da talabijin da satalayet da teburin cin abinci da kujerin kushin guda uku da teburin ajiye kwamfuta da na ajiye takardu. Can gefe kuma ga wani katon teburi dauke da kayan shayi; madara, Lipton din kasar da sukari da wani tebur da ke dauke da tangarare da kofuna iri-iri. Can kuma gaba wani dan sito da kantocin ajiye takalma da wurin sagale kayayyakin sawa da na ajiye jakunkuna ko akwatuna ne. Idan ka fita waje kuma daga siton ga bayan gida da kwamin wanka da shawa da wurin ba-haya da tawu-tawul sun kai takwas da sabulai da man wanka da na shafawa da sauran karikitan bayan gida, ga manya-manyan madubai ko’ina suna kallona.

Bayan na gama zagaye don in san masaukina sosai na kusan wata uku, sai na dawo cikin dakin kwanan na kwance jaka, na bude akwati na shirya komai da komai, na shiga bayan gida na yi wanka da  ruwan zafi domin kuwa da birnin na Landan da dan sanyi duk da cewa wai ba a fara sanyin ba sosai.

Na fito na ga lokacin Sallar Magariba ya yi, na sha shayi tunda dama da azumi na iso, na koma kan gado ina tunanin ga ni a Landan sai kuma me? Na kunna talabijin na ga yana dauke da tasoshi kusan 63, na yi dariya na ce ai ba shawarakanci ya kawo ni ba da zan tsaya kallo kullum rana ta Allah. Na shiga latsa wannan tasha, ina kamo waccan sai da na gano dukan tasoshin, sa’annan na shiga tunani, nan ne kuma zan yi zama na tsawon WATA 3 ba mata, ba ’ya’ya, ba ’yan uwa…sai kurum na yi ajiyar zuciya.

Safiya na yi na shirya, na kama hanyar zuwa ga wadanda suka kawo ni Landan, domin mu gana. Ba dai kwadago na zo yi ba. Ba yawon shakatawa ba. Ba kuma hutu ba. Na san kila mai karatu ya ce to me ya kai ka Landan? A tsawon rayuwata ni dai ban san wata sana’a ba fa ce koyarwa, sai kuwa aikin jarida da nake sha’awa, nake kuma tabawa daga lokaci zuwa lokaci. Malanta ita nake yi a matsayin aikina na rayuwa, aikin jarida kuwa rayuwata ce, ba na iya barinsa ko da ba ni da aikin yi. Amma ba aikin jaridar ya kawo ni Landan ba, malantar ce!

Za mu ci gaba