Da Dumi Dumi

Asirin Masana’antar Jarirai a Ogun ya tuno

Asirin Masana’antar Jarirai a Ogun ya tuno
Asirin Masana’antar Jarirai a Ogun ya tuno

A ranar Juma’ar makon jiya ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta gano wani gida a yankin Mowe a Karamar Hukumar Obafemi Owode a jihar wanda aka mayar a matsayin Masana’antar Kyankyasar Jarirai.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa  asirin gidan ya tuno ne bayan da daya daga cikin matan da aka tsare a gidan ta kubuta kuma ta sanar wa jami’ansu  a ofishinsu da ke yankin Mowe inda ta shaida musu cewa wata mace da ke mallakar gidan mai suna Florence Ogbonna ce  ta yaudare ta ta kuma tursasa mata zama a gidan inda aka tara mata take kuma yin hayar maza majiya karfi suna lalata da su har su yi musu ciki, idan suka haife sai mai gidan ta karbe jariran, ba tare da iyayensu sun san inda ake kai su ba.

DSP Oyyemi ya ci gaba da cewa “Bayan ta shaida wa jami’anmu wannan lamari ne sai DPO din yankin Mowe, SP Marbis Jayeola ya jagoranci ’yan sanda suka je gidan suka kuma  gano mata 12 masu shekara 20 zuwa 25 wadanda shida daga cikinsu ke dauke da juna biyu kuma suna dab da haihuwa,” inji shi.

Ya ce an kama wadanda ake zargi da gudanar da gidann kyankyasar jariran da suka hada da Misis Florence Ogbonna mai gidan da wadansu maza  biyu  Chibuke Akabueze da Chibuzor Okafor. “Zuwa yanzu ana kula da lafiyar wadanda aka kubutar daga gidan kafin a mika su ga danginsu a daidai lokacin da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kenneth Ebrimson ya bada umarnin tura wandanda ake zargi Sashin Binciken Manyan Laifuffuka  inda ake bincikar su kafin a gurfanar da su a gaban kotu,” inji shi.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya