Da Dumi Dumi

Asisat Oshoala da Sadio Mane sun lashe Gwarazan ’yan kwallon Afirka

‘Yar wasan Najeriya da kungiyar Barcelona, Asisat Oshoala ta lashe Gwarzuwar ’yar kwallon Afirka karo na hudu bayan ta doke Ajara Nchout ta Kamaru da Thembi Kgatlana ta Afirka ta Kudu.

Lashe wannan kyautar ya sanya ta yi daidai da tsohuwar ’yar wasan Najeriya Perpetua Nkwocha wadda ita ma ta lashe kyautar sau hudu. Kuma su kadai ne suka taba samun kyautar sau hudu a tarihi.

Hakanan kuma, dan wasan Senegal da Liverpool Sadio Mane ne ya lashe Gwarzon dan kwallon na bara bayan ya doke Mohammed Salah da Riyadh Mahrez.

Sai dai Achraf Hakimi dan wasan Moroko da Dortmund ne ya doke ‘yan wasan Najeriya guda biyu; Victor Osimhen and Samuel Chukweze wajen lashe Gwarzon Matashin dan kwallon Afirka.

ADVERTISEMENT
Share