✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta mika wuya ga bukatun ASUU kan IPPIS

Gwamnati ta tsame malaman daga IPPIS kuma za ta ba su biliyan N65 domin biyan bukatunsu.

Gwamnatin Tarayya ta amince da tsame malaman jami’a daga cikin ma’aikatan da za ta rika biya a karkashin tsarin albashin bai-daya ana IPPIS.

A tattaunawar sulhunta da kungiyar malaman jami’a ta ASUU, gwamnati ta amince ta biya su albashin watan Fabrairu zuwa Yuni da suke binta bashi a bisa tsarin GIFMIS.

Da yake magana bayan tattaunawarsu ta kusan awa bakwai, Ministan Kwadago, Chris Ngige ya ce, gwamnatin ta amince ta akwaya yawan kudaden da za ta ba malaman daga Naira biliyan 50 zuwa biliyan N60.

Ya ce an kara yawan alawus dinsu daga biliyan N30 zuwa biliyan N35 sai kuma kudaden gyare-gyare da aka kara zuwa biliyan N25 daga Nairab biliyan 20.