✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ASUU ta musanta janye yajin aiki

ASUU ta ce duk wani shafin Twitter mai dauke da sunanta ungulu ce da kan zabo

Kungiyar Malaman Jami’a a Najeriya (ASUU) ta musanta cewa ta janye yajin aikin da ta kwashe wata da watanni tana yi.

Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, da shugaban reshenta na Yankin Babban Birnin Tarayya, Dokta Ben Ugheoke, suka tabbatar da haka ga wakilinmu ta wayar tarho.

Tun da farko dai mun yi kuskuren bayar da labarin cewa malaman jami’ar sun janye yajin aikin da suke yi kamar yadda muka gani a wani shafin Twitter mai dauke da sunan kungiyar.

Sai dai shugabannin na ASUU sun ce babu abin da ya hada su da shafin.

Sun ce duk shafukan da ke da sunan ASUU na ungulu da kan zabo ne, domin kungiyar ba ta da shafin Twitter.

Tuntubar shiyyoyi

Sun kuma jaddada matsayin da suka bayyana ranar Juma’a, cewa suna bukatar kwanaki biyar zuwa shida don tuntubar rassan kungiyar na shiyyoyi.

Bayan jin ta-bakin shiyyoyin a kan tayin da gwamnati ta yi musu ne, a cewarsu, za su dawo ranar Juma’a mai zuwa don sanar da hukumomi shawararsu a kan ko za su ci gaba da yajin aikin ko za su janye.

Ranar Juma’a ne dai Gwamnatin Tarayya ta mika wuya ga malaman jami’ar, ta amince ta cire su daga kan tsarin biyan albashi na IPPIS.

Gwamnatin ta kuma yarda ta biya su albashinsu tun daga watan Yuni.

An dade ana ruwa

Yanzu dai an kusa kwashe kwana 255 akasarin jami’o’in Najeriya na rufe sakamakon mamayar annobar COVID-19 da yajin aikin kungiyar ASUU.

Kungiyar ta ASUU ta sha fadawa yajin aiki da nufin tilasta wa gwamnati daukar wadansu matakai wadanda ta kan ce za su inganta ilimi a kasa.

Sai dai kuma a lokuta da dama gwamnati kan yi turjiya bisa dalilai da dama ciki har da rashin kudin da za a dauki matakan da kungiyar ke bukata.