Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Atiku da PDP sun gabatar da takardun sakamakon zaben Neja, Yobe

Jam’iyyar adawa ta PDP da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Atiku Abubakar, sun gabatar da takardun sakamabon zaben shugaban kasar Najeriya da aka yin a ranar 23 ga Fabrairu 2019.

Hakan ya biyo bayan ci gaba da ake yi na sauraran karar da jam’iyyar PDP da dan takarar shugaban kasar suka shigar, inda suka gabatar takardar rubuta sakamakon zabe ta Hukumar zabe INEC ta EC8C, EC8B da EC8A. wadanda aka yi amfani da su a mazabun Kananan Hukumomin jihohin Neja da Yobe lokacin kada kuri’a.

ADVERTISEMENT

Lauyoyin Atiku da PDP, Farfesa Ben Nwabueze (SAN) da Levy Uzoukwu (SAN), ne suke jagorantar shari’ar kuma sun bukaci kotu ta ba su izinin ci gaba da gabatar da wasu shaidu.

ADVERTISEMENT