✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atiku ya kai Buhari Kotun Koli

Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Alhaji Atiku Abubakar ya garzaya Kotun Koli yana kalubalantar hukuncin da Kotun Sauraren…

Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Alhaji Atiku Abubakar ya garzaya Kotun Koli yana kalubalantar hukuncin da Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa ta yanke, inda ta ba Shugaba Muhammadu Buhari nasara.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Abubakar yana kalubalantar shari’ar kotun ce wadda daukacin alkalan kotun suka yi watsi da karar da Jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar suka shigar gabanta suna kalubalantar nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC ya samu a zaben da aka gudanar a watan Fabrairun bana.

Tun bayan yanke hukuncin ne, Atiku Abubakar yake ta tattaunawa da lauyoyinsa domin daukaka karar, inda  yake da mako biyu domin ya daukaka karar tasa zuwa Kotun Koli, idan bai gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba. Kuma a ranar Talatar da ta gabata ce Atiku ya kai Muhammadu Buhari da Jam’iyyarsa ta APC  Kotun Kolin.

Daya daga cikin lauyoyin dan takarar PDP ya ce sun tattaro akalla hujjoji 70 da za su sake gabatarwa gaban Kotun Koli a kan kura-kuran da alkalan kotun baya suka yi a shari’ar.

Shigar da karar yanzu ya zama dole alkalai su yanke hukunci cikin wata biyu. Lauyan ya ce hujjoji masu karfi za su gabatar a gaban kotun, wacce ita ce kotun karshe wajen yanke hukunci.

Daga cikin batutuwan da lauyoyin za su tabo a Kotun Kolin sun hada da yadda shaidar da Buhari ya gabatar, Janar Paul Tarfa ya zo gaban kotu ya musanta abin da Shugaban Kasar ya fada a baya. Haka zalika lauyoyin Atiku za su hakikance kan takardar kammala sakandaren ta Shugaba Buhari inda suka ce an samu tufka da warwara a tsakanin takardun Cambridge da na WAEC. Lauyoyin dan takarar Jam’iyyar PDP din sun koka da yadda aka yi watsi da duk karar da suka gabatar a gaban waccan kotu.