Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Atiku ya yi alakawarin inganta noma da kasuwanci idan aka zabe shi

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasar Najeriya a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya yi alkawarin inganta noma da harkokin kasuwanci idan aka zabe a matsayin shugaban kasar Najejriya.

Dan takarar ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da yakin neman zabensa a filin wasa na Sani Abacha jihar Kano. Atiku  ya bayyana irin rashin jin dadinsa game da durkushewar masana’antu a  duk fadin Najeriya kuma ya dauki alwashin farfado da su idan har ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya.

ADVERTISEMENT