✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atiku ya yi kira ga Buhari a kan masu zanga-zangar #EndSARS

Yin amfani da karfin tsiya babu abin da zai haifar sai harzuka lamarin a madadin ya shawo kansa.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya gargadi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ta daina amfani da karfin tsiya ta kowace siga wajen korar masu zanga-zangar kyamar rundunar SARS.

Atiku wanda ya yi takarar shugabancin kasar nan a jam’iyyar PDP, ya bayyana gargadinsa ne cikin wani sako da ya wallafa a shafukansa na Twitter da Facebook.

Wazirin Adamawa ya kuma bayyana damuwa a kan mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar zangar-zangar da ta rikide ta koma rikici a wasu sassan kasar.

Ya ce, “Kira na ga gwamnatin da Buhari ke jagoranta shi ne kada ta raya mata cewa sai ta yi amfani da karfin tsiya a kan masu zanga-zangar #EndSARS.”

“Masu zanga-zangar EndSARS su na da manufa, don sun yi abin da ya dace kuma wannan shi ne lokaci mafi dace da ya kamata a duba lamarin domin gaggauta biyan bukatunsu.”

“Yin amfani da karfin tsiya babu abin da zai haifar sai harzuka lamarin a madadin ya shawo kansa,”inji Atiku.

Ya kara da cewa, “Idan gwamnati ta nuna damuwarta a kan lamarin, al’umma za su rusuna don yanzu lokaci ne da ya kamata a yi amfani da hankali da basira ba wai karfi da yaji ba.”

Ya kuma nemi Shugaba Buhari da ya fito ya gabatar da jawaban rarrashi ga ’yan kasa musamman matasa.