Da Dumi Dumi

Audu-mugu: kidayar ingarmar Rano

Direban alli na horon dalibai da yin kidayar ingarmar RanoAudu-mugu, shi ne shugaban Hukumar kididdige yawan al’ummar kasar Haurobiya, wanda a halin yanzu yak eta fafutikar sukar duk wata kididdiga da aka taba yi a kasar Haurobiya. Wannan mugun daji, ya bayyana cewa kididdigar zamanin Baba-Ojo duk kirkira alkaluman aka yi. Saboda kwakyariyar Audu-mugu har abokan kwadagonsa sun fara takun saka da shi. Manufar Audu-mugu ita ce kidayar ingarmar Rano, wato da matacce da rayayye, ta yadda zai samu ya kara adadin mutanen kauyensu, har yawansu ya zarce na Arewatawan Haurobiya.
Audu-mugu, tsohon manajan Kamfanin sarrafa barasa, shi yasa ma da aka baje masa jaddawalin kididdigar al’ummar Haurobiya, sai kawai ya karkata na-mujiyarsa, ya rika yi wa alkaluman kallon ruduwa. Don haka da barasa ta gaya masa waskiya, sai kawai ya yunkura wajen yki da daukcin alkaluman kididdigar da aka yi tun da aka kafa kasar Haurobiya.
Lallai Haurobiyawa ya kamata ku yi wa Shugaba Jatau Mai-sa-in-sa godiya da ya nada muku Manajan Daraktan Kamfanin Birkita kwakwale a matsayin babban Jami’in kididdiga na kasar Haurobiya. Kun ga shi a firgice yake, don haka yake son firgita kowa. Haurobiya a daina ja-in-ja da mugu, domin ya samu galaba wajen aiwatar da kidayar ingarman Rano, ai sai kawai a ce wa In-gwangwaje-in-wala da Gwamnan Asusun karfanfana da Shugaban Hukumar Zabi-sonka, ku je ku yin a-kasa, har ku kasa, mugu kuwa ya kasa ya kwashi kashi.
A matsayina na Direban Allin wannan farfajiya ta Dodorido da ke Amintattar jaridar kasar Haurobiya, ina ganin Gwamnatin Jatau Mai-sa-in-sa ta daina salwantar da dukiyar al’umma wajen daukar gwanayen kididdiga, domin tana da gwani na gwanaye, wanda zai shirya mata kyakkyawar shiririta baje-kolin Hauro a kowace shekara; zai kuma nuna salo wajen jirkita jaddawalin damin Hauron da ke Babban Asusun Haurobiya; uwa-uba ba sai kun kada kuri’u ba, da zarar zabi-sonka ya karato shi zai iya kirkira muku alkaluman kuri’un da suka dace Haurobiyawa su kada. Ya kuma yi muku zaben tumun dare, ta yadda duk wanda yake ganin ya fi cancanta shi zai jibga wa kuri’u.
Da kyau Audu-mugu, ka kara kwazo, musaman idan ka kwankwadi ruwan Karen-barau ko gwalolon dauda da sauran na’ukan barasa da Kamfaninka ke sarrafawa. Haurobiyawa manhajar kidaya a Haurobiya ta koma ta ingarmar Rano.

Jaje

Assalamu alaikum warahmatullah.
Bayan gaisuwa irin ta masu fuskantar alkibla, ina fatan an yi bukukuwan sallah lafiya, kama ina fatan dalibai sun ari takalman Mallam Tunau akan irin darasin da muka biya a makon da ya arce.
Bayan haka ‘yan uwana dalibai ina mika sakon jaje na ga babban direban direban allinmu, akan ziyarar da bakin da ba’a son zuwansu,suka yi har gidansa. A cikin kwanakin da suka arce. Ina rokon Mai duka ya kiyaye gaba  amin.
Daga Mataimakin Saka-katare na Jihar Tumbin Giwa, Hlliru Kabir Gogel. 08039336748

ADVERTISEMENT
Share