✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aune-aune da gwaje-gwace domin kiwon lafiya

Likita, kana yawan magana a kan idan an je asibiti a tabbata an yi wa mutum gwaje-gwaje da aune-aune kafin a ba shi magani, ko…

Likita, kana yawan magana a kan idan an je asibiti a tabbata an yi wa mutum gwaje-gwaje da aune-aune kafin a ba shi magani, ko wabanne irin aune-aune ne wabannan?

 

Amsa: Kwarai kuwa duk asibitin da mutum ya ziyarta da matsala ta lafiya yana da kyau kafin a ba shi magani a yi masa ’yan tambayoyi, a kuma yi masa aune-aune a jikinsa, sa’annan idan ta kama a yi gwaje-gwaje. A wasu lokuta irin aune-aunen da likita zai yi a jikin mutum suna danganta ne da matsalar da mutum ya zo da ita da kuma kwarewar likitan. Duk da haka dai akwai aune-aune da suka zama wajibi, wato dole a yi wa mutum kusan tun kafin ma ya shiga bakin ganin likita.

Wabannan aune-aune ke nan tun a wurin masu jinya a kan fara su, kuma sun haba da:

1. Bumin jiki: Akwai cututtukan da sukan zo da zazzabi, wanda idan an auna da na’urar bumin jiki yakan nuna cewa akwai zazzabin ko a’a.

2. Aikin zuciya: Wannan na nufin awon yawan aikin da zuciya ke yi a cikin minti guda. A mafi yawan lokuta rashin lafiya daban-daban kan kara wa zuciya aiki.

3. Bugun jini: Shi kuma yana nufin auna karfin aikin da zuciya kan yi na harba jini sassan jiki. A mafi yawan lokuta akan samu shi kuma wannan ya yi kasa a maras lafiya.

4. Yawan numfashi: Shi ma na nufin auna yawan numfashin da maras lafiya yakan yi a kowane minti baya. Wato zai iya yin yawa ko kuma ya yi kaban.

5. Yawan karfin iskar obygen: Wannan ma akan auna shi idan mutum ya samu matsalar hanyoyin numfashi ko hanyoyin magudanan jini, amma ba a ko’ina ake iya auna shi ba, saboda ba kowane asibiti ke da kayan awon ba.

6. Tsayi da nauyi: Wannan awo kan yi nuni da irin yawan kibar mutum, domin a irin wannan zamani cututtuka da dama na samun shiga jikin da ke da kiba, misali irin su ciwon hawan jini, da na zuciya, da na sanyin kashi da na bugun jini a kwakwalwa, wato irin mai sa mutuwar barin jiki bin nan.

To a wurin likita kuma wani likitan yakan tusa abin da masu jinya suka auna, ko kuma ya bora nasa binciken bayan ya yi ’yan tambayoyi. Nasa aune-aunen sukan ta’allaka a kan abin da marar lafiya ya zo da shi. Misali, idan ciwon ciki ne, likita zai fi mai da hankali a kan dubawa da aune-aunen da suka shafi ciki. Amma akan iya ganin wani abu mai kama da akasi; a ga likita ya duba wani wuri da ba a yi korafi a kansa ba. Misali, idan aka zo da matsalar ciwon ciki za a ga bayan cikin ana duba idanuwa ko farata, duk da cewa idanu ba ciki ba ne. Abin da ya sa shi ne cewa matsalolin ciki kamar na hanta za su iya nunawa a ido ko a farata. Ko kuma namiji ya je da matsalar fitsari a duba hanyar bayan-gida, tun da a maza a nan aka fi samun matsalolin fitsari. A wasu lokuta kuma likita da ya yi ido hubu da matsalar zai san mece ce, misali idan kuraje ne mutum ya je da su, likitan fata da ya gan su ya san ko wabanne iri ne, yawanci ba sai ya kara bata lokacinsa a kan sauran binciken ba, musamman idan akwai layin masu jira.

Ban da irin wabannan sauran abubuwan da likita kan duba sun haba da:

1. Idanuwa: Inda muka ce akan iya duba wasu matsaloli kamar na hanta da matsarmama, inda ido kan nuna alamun shawara. Ko kuma ya duba ko akwai karancin jini a jiki, wanda ta ido ma ana iya ganewa.

2. Baki da hakora: a ga lafiyar baki da ta hakoran ko ma ciwon ya taba lafiyar bakin ko hakora ko dasashi ko harshe.

3. Kirji da numfashi: Likita yakan sa abin jin numfashi a kirji a bangarori da dama domin jin irin numfashi da irin aikin da zuciya take yi a wannan lokaci

4. Bugun jini: Sai kuma ya auna hawan jini ko akwai, ko kuma ya duba ko bugun jinin raguwa ya yi.

5. Hannaye da Farata: akwai wasu cututtuka da kan nuna alamu a tafin hannuwa da farata wanda da likita ya gani zai san akwai matsalar, misalansu su ne ciwon karancin jini da ciwon hanta.

6. Kafafu: Su ma kafafu kan yi nuni da wata matsala ta jiki. Misali ciwon zuciya ko na hanta ko na koda kan zo da kumburi a kafa wanda da likita ya gani ya latsa, ya san irin matsalar.

Akwai kuma wasu karin nau’in aune-aune da dama da likita kan zaba ya yi, wabanda kuma ba a zayyana su a sama ba. Misali kamar na masu juna biyu, wanda awo ne na musamman da muka taba bayani a nan. Akwai kuma wabanda likita ne zai yi su domin matsalar da maras lafiya ya zo da ita, misali duba mace ko ma namiji duba na sirri ko na kusanci dangane da irin ciwon da aka je masa da su.