Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Aune-aune da gwaje-gwaje domin kiwon lafiya (2)

Bayan mun duba aune-aunen jiki da ma’aikatan lafiya kan yi a makon jiya, a yau kuma za mu duba gwaje-gwaje. Su kuma gwaje-gwaje su ne binciken da ake yi idan an debi wani abu a jikin mutum domin neman ciwo. Gwaje-gwajen lafiya, duk da cewa a mafi yawan lokuta suna da tsada, sukan zamo masu amfani wajen gano takamaiman ciwon da yake damun mutum. Maimakon a yi ta dirkar magunguna barkatai da ka, gwaji shi ne zai nuna ainihin ciwo tashi guda, wanda hakan zai sa a ba da maganin wannan ciwo kadai ba tare da an wahalar da marar lafiya ba.

Abubuwan da akan gwada a jikin mutum sun hada da jini da fitsari da majina da bayan gida, yanki ko sashen wani ciwo ko gyambo ko kari ko tsuro. Bayan wadannan kuma akwai hotuna iri-iri na jiki da akan iya dauka domin nemo ciwo. Wadannan sun hada da hotunan D-ray da na ultrasound da na MRI da na CT da Echo da sauransu. Bari mu dauki wasu daga ciki mu ga me akan gano idan an gwada su:

ADVERTISEMENT

 

1.        Jini: Gwajin jini shi ne kan gaba wajen gwaje-gwajen lafiya. A jini akan iya gano cututtuka barkatai, tun daga kwayoyin cuta masu sa zazzabin cizon sauro da na typhoid da sauran kwayoyin cuta, har zuwa gano karancin sinadarai ko yawansu a cututtuka irin na koda ko hanta ko zuciya ko makoko, ko awon suga domin neman ciwon suga. Akan iya auna yawan jini shi kansa a gano ko marar lafiya na dauke da karancin jini, ko a nemo ajin jinin mutum. Kai har kananan kwayoyin halitta na jiki na DNA ana iya aunawa a gano wani ciwo ta gwajin jini

ADVERTISEMENT

 

2.        Fitsari: Shi ma ana iya gwada shi domin binciken cututtukan jiki daban-daban tun daga na ita kanta kodar mai sarrafa fitsarin, zuwa sinadaran da kan nuna ciwon hanta, har na kwayoyin cuta irin su shigar kwayoyin cuta a mafitsara. Ana ma iya awon sinadarai kamar suga a cikin fitsarin, wanda yawansa a fitsarin kan yi nuni da ciwon suga. Akwai ma kwayoyin halittu da za a iya aunawa wadanda za su iya yin nuni da wasu manyan cututtuka irin su ciwon daji.

 

3.        Bayan Gida: Akan yi shi idan mutum na fama da yawan ciwon ciki domin gano ko akwai macijin ciki, inda akan gano kwayayen macizan, ko a duba jini a bayan gida ga masu ciwon olsa domin a kiyasta ko olsa na zubar da jini. Haka nan ma ta awon bayan-gida akan iya gano manyan cututtuka irin su ciwon daji na babban hanji.

 

4.        Majina: A majina ma akan iya gano cututtuka na huhu da dama, tun daga ciwon tarin numoniya zuwa na TB, zuwa gwajin kwayoyin ciwon daji na huhu da sauransu

 

5.        Hotuna: Suna bayyana cututtuka daban-daban da ke jiki tun daga kumburi zuwa kari, zuwa daji, zuwa taruwar jini ko ruwa a wani sashe na jiki. Ban da cututtuka ko da an samu akasi an ci ko an hadiye wani abu da bai kamata a ci ba, hotuna sukan nuna inda abin ya shiga ya makale. A wasu lokuta hotunan ma da kyamara ake dauka, kamar hoton ciki da ake wa masu ciwon gyambon ciki domin gano ko akwai olsar ko babu.

 

Ni ina da ciwon olsa ne. Da ya tashi na je asibiti aka kwantar da ni na kwana hudu. An sallame ni ina shan magunguna amma har yanzu akwai ciwon kirji. Ko mene ne dalili?

Daga Amina A.M

Amsa: Tunda fari yaya aka yi aka san ciwon olsa ne da ke? An yi gwaji an tabbatar? Domin a wasu lokuta matsalar ciwon kirji a zuciya ne fa ba a ciki ba. Don haka ne ko an sha maganin ciwon olsa, in dai ba ciwon ba ne ba za a samu sauki ba. A wasu lokutan kuma ciwon ne da gaske, amma magungunan da aka yi amfani da su su kasance na jabu.

 

Ko ciwon olsa na daya daga cikin cututtukan da akan gada?

Daga Dauda Mani

Amsa: A’a, ciwon gyambon ciki ba ya daga cikin cututtukan da akan iya gado ko a dauka daga wani. Kawai dai wadansu ne suke da rashin sa’a cewa bangon cikinsu ba ya da kwari, nan da nan zai yi gyambo kamar yadda fatar jiki ke saurin jin ciwo a wadansu.

 

Na yi rashin lafiya da aka gwada jinina aka ce ina da suga na dauki matakin yaki da shi. Da na ji sauki ban kara kula batun ba, to shin ko akwai matsala?

Daga Murtala Ahmad, Gusau

Amsa: A’a, ai Malam Murtala in dai aka gwada aka ce akwai suga ba za ka manta da maganar ba. Kamata ya yi ka yi bibiya a kan gwajin, wato ka rika zuwa duk bayan watanni ana aunawa a gani ko ya tafi, musamman  idan a danginka akwai mai ciwon suga, ko kuma idan kai mai kiba ne. Bayan an kara aunawa sau biyu zuwa uku aka ga ya sauka to shi ne za ka manta da batun, amma idan ba ya sauka ba, to watakila sai ta kai ga fara shan magani, dangane da tarihin ciwon a gidanku ko kibarka. Likitan da ke bibiyar awon da gwajin shi za ka samu ya rika ba ka shawara a kan wane mataki ne ya dace da kai.