✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Auren Hanan: Aisha Buhari ta fusata da zanen barkwanci

Auren diyata ba rashin damuwa da halin da 'yan kasa ke ciki ba ne; babu adalci

Mai dakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Aisha ta mayar da martani game da zane barkwancin bikin diyarta Hanan, wanda ya karade shafukan zumunta tare da jawo surutai.

Zane barkwancin na jaridar Daily Trust wanda Mustapha Bulama ya yi an nuna Aisha Buhari rike da hoton daurin auren diyarta ga ‘yan Najerriya suna nutsewa a kogi.

Kakakin Aisha Buhari, Barista Alyu Abdullahi a zantawarsa da BBC kan batun ya ce ‘ya’yan shugabanni na da ‘yancin yin aure idan lokaci ya yi ba sai jama’a na jin dadin mulkin shugabannin ba.

“Zanen barkwancin na Mustapha Bulama da ke yawo bai yi adalci ba, domin daurin aure ba ya cikin alamun nuna rashin damuwa da halin da ‘yan Najeriya ke ciki.

“Hakikanin gaskiya, abubuwa irin wadannan ne suka sa Matar Shugaban Kasa ta gana da ma’aikatanta a watan jiya, inda ta shaida mana cewa tana so bikin ya kasance ba a tara jama’a ba, kuma babu babban biki.

Barista Aliyu ya kara da cewa, “hotunan ma’auratan da Aisha Buhari ta sanya a shafukan zumunta, ta sanya ne domin ta yi godiya ga masu fatan alheri, ba don ta ci mutucin ‘yan Najeriya ba.

“Zan iya cewa daurin auren Hanan Buhari na daga ciki wadanda aka fi yi ba tare da mutane sosai ba a Najeriya”.

Aisha Buhari ta sanya hotunan shirye-shiryen daurin auren Hanan da angonta Turad a ranar Juma’a

Ya ce bidiyon da ke yawo na shagalin bikin ma’auratan inda ake musu liki da kudi a yayin da suke rawa, ba a Fadar Shugaban Kasa aka dauka ba, an yi ne a Kaduna, bayan an kai amaryar a gidan surukanta.

Ya ce Uwargidar Shugaban Kasa na sane da ka’idodin COVID-19 da aka sanya don haka ne ta tabbatar da dukkanin mahalarta sun kiyaye dokokin.

Aisha Buhari ta sanya hotunan shirye-shiryen daurin auren Hanan da angonta Turad a ranar Juma’a

A ranar Juma’a 4 ga Satumba 2020 ne Aminiya ta kawo labarin bikin Hanan Buhari jim kadan bayan Aisha Buhari ta wallafa hoton ma’auratan.

Wasu sun yi ta korafi cewa bikin ya zo a lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da matsin tattalin arziki da kuma annobar coronavirus.