✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Awon igiya a Kano

Gida wuri ne da ya kunshi dakin kwana da ban-daki da dakin baki da kuma farfajiya domin shakatawa. Idan kuma ka fito wajen kofar gidan…

Gida wuri ne da ya kunshi dakin kwana da ban-daki da dakin baki da kuma farfajiya domin shakatawa. Idan kuma ka fito wajen kofar gidan ana bukatar isasshiyar hanyar wucewa.

Awon igiya wani tsarin gidaje ne wanda ya kunshi kowa ya yi tsarin gininsa yadda ya ga dama, wato ko dai gidan sama ko mai dakuna barkatai ba tare da duba yanayin  kasar ko za ta dauki gidan sama ballantana akasin haka ba, idan aka zo maganar masai (sokawe) za ka iya yin ta a kofar gidanka ko in ce a ‘kan hanya’ ba tare da lura da jama’a na wucewa ba.

Wani bangaren irin wadannan unguwanni za ka ga layi ba ya bullewa ko kuma abin hawa kamar mota da bubur ba sa iya wucewa. Idan kuma cuta wadda ake bukatar  abin hawa ta faru sai dai a dauki marasa lafiya a hannu ko tabarma. Lura da matsalolin zamani sun fi faruwa ne a ire-iren wadannan unguwannin saboda cinkoso da karancin hanyar da za a kai dauki na magani da kuma tsaro akwai bukatar mu yi gyara.

Kowane birni yana da tsarin gidajen zama kashi-kashi wanda ya kunshi gidajen gwamnati da na ma’aikata da ’yan kasuwa da kuma masu karamin karfi.

Unguwanni sun kasu ne dangane da tsarinsu kamar; kebantattun gidaje (GRA) su ne wadanda tsarinsu ya kunshi akasarin ma’aikatan gwamnati. Sai kuma tsarin gidajen da gwamnati ta yarda da su wato awon gwamnati, su kuma sun kunshi layuka yalwatattu wadanda za ka iya samun ma’aikatan gwamanti da na kamfani da ’yan kasuwa. Sai kuma tsari na uku wato awon igiya. Wannan tsari za ka iya samun mutane masu karamin karfi wadanda matsalar rayuwa ta sa ba su da zabin wurin zama, yawancinsu sun fi fama da matsalar kula daga gwamnati da kuma tarin laifuffuka wanda aka iya jefa kananan yara cikin kowanne hali mara dadi.

A Jihar Kano akwai unguwanni da dama wadanda aka gina su a kan tsarin awon igiya inda za ka ga suna da karancin abubuwan more rayuwa kamar babban asibiti da makaranta da manyan tituna da sauransu. Matsalar tarbiyya na daya daga cikin abubuwan da suka addabi wadannan unguwanni saboda akwai wuraren da za ka zo ko jami’an tsaro ba sa samun damar shiga da abin hawa,  sannan idan aka duba shekarun baya lokacin aka yi fama da cutar amai da gudawa ta fi yaduwa a unguwannin awon igiya saboda karancin magudanun ruwa da hanyoyi.

Unguwannin awon igiya suna samuwa ne sakamakon kawar da kai ko rashin sanin jami’an tsara gidaje  a lokacin da za a yanka filaye. Yawancin masu iko da wuraren ba su damu da me zai faru daga baya ba, kamar cinkoso da rashin yalwatacciyar  hanya.

Unguwanni kamar; Kurna da Sheka da Birged da Dorayi da wasu a cikin tsohon birni  da wasu ma da ban iya kawo su ba, za ka same su da irin matsalolin cinkoso dalilin awon igiya. Dalilan da suke kawo aukuwar awon igiya suna da yawa amma idan aka duba masu sayen filayen suna yi ne domin guje wa matsalolin gidan haya da tsangwamar masu gidajen a wasu wuraren har ma da jama’ar gari idan suka fuskanci cewa mutum haya yake yi, to darajarsa ba kamar mai gidan kansa ba ne.

Magance matsalolin cinkushewar unguwannin sun rataya ne a kan gwamnati da kungiyoyin dillalai da jama’ar gari. Za ka gamsu da dalilaina kamar haka:

Gwamnati da Majalisar Kano suna da hakki na kafa doka ko gyarata don taimakawa wajen hana unguwannin awon igiya ta hanyar tilasta wa masu yanka filaye bin ka’idojin tsara birane. Kungiyoyin dillalai  suna da nasu hakkin wajen yin rajista da gwamnati domin tallafa musu da yadda za a tsara biranen, tare da hukunta duk wanda ya saba wa tsarin kungiyar. Haka jama’ar gari na da rawar takawa wajen bijire wa duk wanda ya yanka filayen awon igiya a ko’ina.

Idan akwai dokar da ta hana to lallai akwai bukatar gwamnati ta zage dantse wajen kula da sababbin unguwannin da  ake yi a yanzu domin kauce wa matsalolin awon igiya.

Mustapha Garba Kiru (Danmuji), Kano

08033503662

Gmail: [email protected]