✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ayyukan jinkai babban aikin da ke gaban  Minista

Kungiyar  Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa Najeriya ce ta biyar a cikin kasashen da suke da matsalolin jinkai a duniya, inda take tafiya…

Kungiyar  Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa Najeriya ce ta biyar a cikin kasashen da suke da matsalolin jinkai a duniya, inda take tafiya kafada-da-kafada da kasashe irin su Yemen da Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Kongo da Sudan ta Kudu da kuma Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya da Afghanistan da sauran kasashe da rikici ya daidaita su.

Shugaban Kwamitin Red Cross, Mista Peter Maurer shi ya bayyana wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari haka a birnin Abuja a ranar Talatar da ta gabata. Ya ce kamarin wannan lamari a Najeriya ya sa yara kananan da dama ba su san inda iyayensu suke  ba, kuma ba su ma san daga ina suka fito ba.

Bisa irin wannan hali da Najeriya take ciki, ya zama akwai babban kalubale ga sabuwar Ministar Kula da Ayyukan Jinkai da Ci gaban Al’umma, Hajiya Sadiya Umar Faruk. Matsalar da ke tattare da kalubale da ayyukan ta’addanci da fashi da makami da rikicin manoma da makiyaya da rikicin kabilanci da sauran laifuffuka da ake aikatawa  kai-tsaye suke shafar jama’a da dama ko suke jefa su cikin halin kaka-ni-ka-yi. Mun jinjina wa Gwamnatin Buhari domin samar da wannan ma’aikata, wanda tamkar kwaikwayo ne daga kasashe irin su China, Sudan, Jamhuriyyar Nijar, Sudan ta Kudu da kuma Rwanda wadanda suke da irin wadannan ma’aikatu.

A bara rahoton da Babban Kwamishinan Kula da ’Yan Gudun Hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar ya ce akwai ’yan gudun hijira miliyan biyu da dubu 240 a Najeriya, inda wadansu dubu 213 da 179 suke gudun hijira a kasashen Kamaru, Chadi da kuma Nijar. Kwamitin Red Cross tun a watan Janairun bana yake samar da tallafi a kan kiwon lafiya ga mutane sama da dubu 258, baya ga samar da kayan abinci ga ’yan gudun hijira dubu 640. Yanzu babban  aikin da ke gaban Ministar shi ne ta yadda za ta tabbatar da kula da walwalar al’ummar Najeriya da aka raba su da gidajensu kan matsalar rashin tsaro da ta addabi wasu sassan kasar nan, kuma alhakin yin hakan ya dogara a kan wannan ma’aikata.

Babu wani tabbataccen tsari da gwamanti ta yi kan wannan ma’aikata, amma yanzu ya zama dole a tabbatar an samar da tsare-tsare da kuma fitar da ayyukan ma’aikatar. Mafi muhimmanci kasafin kudin da za a ba ta, dole ne a tabbatar an bada shi cikin gaggawa, akwai sauran hukumomi da cibiyoyi da suke ayyukan bada agaji ta hanyoyi daban -daban kamar su Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) wadda hukuma ce da take karkashin Fadar Shugaban Kasa, ga Hukumar Kula da ’Yan gudun Hijira da kuma Kwamitin Shugaban Kasa kan Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI) da Gidauniyar Bada Tallafi da ke karkashin Janar Theopihilus Danjuma (mai ritaya). Yana da muhimmanci a sake kula da tsarin ayyukan irin wadannan hukumomi da cibiyoyin bada tallafi, ta yadda za su kasance a karkashin wannan ma’aikata ta jinkai da tallafi da kuma ci gaban al’umma, wanda hakan zai taimaka wajen  maida hankali a kan bada ayyukan jinkai.

Ga Minista akwai bukatar ta tashi cikin gaggawa da tabbatar da samar da adadin ’yan gudun hijira da inda suke, daga ina suka fito da kuma matsugunin da suke na je-ka-na-yi-ka.Wannan hanyar za ta taimaka sosai, don haka muna kira ga Minista ta tabbatar duk matsugunan ’yan gudun hijira da gwamnati ba ta san da su ba, an sa su cikin tsarin, kuma an ba su duk wata kula da ta kamata, babu wani dalili da dan Najeriya da ke  gudun hijira a ce an manta da shi an yi watsi da lamarinsa, bayan irin bala’in da ya auka masa. Dole ne gwamanti ta san a ina suke zama yaya rayuwarsu take kuma a nemo hanyar da za su rika samun tallafi.

Gwamnati ta san cewa ta dora wa wannan ma’aikata babban aiki na kula da kuma kare wadannan bayin Allah da rikici ya raba su da gidajensu da wadanda aka yi garkuwa da su, ko bala’in gobara ya auka musu da sauransu. Akwai ayyuka da dama a gaban Hajiya Sadiya Umar Faruk, wacce ta taba zama Kwamishinar Hukumar Kula da ’Yan gudun Hijira, duk da haka akwai jan aiki a gabanta, wanda dole ta daura damara wajen tafiyar da wannan babban aiki, da kuma karkade wasu hukumomin da cin hanci da rashawa suka yi katutu a cikinsu.

Muna yi mata fatan alheri da samun nasara a kan wannan aiki.